Shugaba Bola Tinubu ya sauke ministoci shida daga cikin ministocinsa a wani bangare na sake fasalin gwamnatinsa da nufin inganta ayyukan gwamnati.
Wadanda aka sauke daga mukaminsu sun hada da ministar harkokin mata, Barr. Uju-Ken Ohanenye; Ministar yawon bude ido, Lola Ade-John; Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman; Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane Abdullahi Muhammad Gwarzo da Ministan Cigaban Matasa Dr. Jamila Bio Ibrahim.
- Yadda Dortmund Ta Barar Da Garinta A Santiago
- Shekarau Ya Fara Jagorantar Sabuwar Tafiyar Kawo Sauyi A Nijeriya
Shugaban ya kuma kori ministar jin kai da aka dakatar, Dr Betta Edu a hukumance.
Wannan sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, ta kuma hada da sauya wa wasu ministoci 10 Ma’aikata da kuma nadin sabbin ministoci bakwai, har zuwa lokacin da majalisar tarayya za ta tabbatar da nadinsu.
Nade-naden na zuwa ne a daidai lokacin da ake kira ga gwamnatin da ta sake inganta ayyukanta don magance matsalolin da ke addabar kasar.
Sabbin ministocin da ma’aikatun su sun hada da Dr. Nentawe Yilwatda, ministar harkokin jin kai da rage talauci; Muhammadu Maigari Dingyadi, ministan kwadago da samar da ayyuka; Bianca Odinaka Odumegwu-Ojukwu, Karamar Ministar Harkokin Waje; Dr. Jumoke Oduwole, Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari; Idi Mukhtar Maiha, Ministan harkokin Dabbobi; Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata, Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane da Dokta Suwaiba Said Ahmad, Karamar Ministan Ilimi.
Shugaba Tinubu ya godewa ministocinsa da ya sallama a kan hidimar da suka yi wa al’umma tare da yi musu fatan alheri a kan ayyukansu na gaba.
Ya kuma jaddada cewa, sabbin ministocin tare da takwarorinsu, dole ne su yi aiki tukuru don yi wa kasa hidima.