Tsohuwar Darakta ta Hukumar Inshorar Najeriya (NSITF), Misis Kemi Nelson, ta rasu tana da shekaru 66.
Nelson, ‘yar siyasa ce a jihar Legas kuma mai ra’ayin jama’a, wadda kuma ta kasance shugabar mata ta shiyyar Kudu Maso Yamma ta jam’iyyar APC, ta rasu a ranar Lahadi.
- An Yi Wa Kasurgumin Dan Bindiga Sarauta A Zamfara
- Yajin Aikin ASUU: Mece Ce Makomar Daliban Jami’o’in Nijeriya? (Ra’ayi)
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Legas, Gboyega Akosile, ne ya bayyana labarin rasuwarta.
Nelson dai ta hannun damar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ce.
Tuni ‘yan siyasa a Nijeriya suka shiga yin ta’aziyya da alhinin rasuwarta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp