A yau Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wasu ababen hawa a hanyar Katsina zuwa Jibia a jihar Katsina, inda suka kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu matafiya da yawa.
Wata majiya ta shaida cewa mutane da dama sun samu raunukan harbin bindiga a lokacin da ‘yan bindigar suka bude wuta kan wata motar bas ta hukumar sufurim jihar Katsina (KSTA) da wasu motoci da ke kan hanyar.
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Mahara 2 A Anambra, Sun Kwato Makamai
- Wata Mata Ta Kashe Mijinta Da Wuka Har Lahira A Adamawa
A cewarsa, direban motar bas din mai lamba KT 14D-58 KT a cikinta ne aka kashe mutane uku yayin harin.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kuma kai farmaki wani kauye mai suna Farun Bala inda suka kuma yi awon gaba da shanu tare da kwashe wasu kayayyaki na mutanen kauyen.
“’Yan bindigar sun tare hanyar Katsina zuwa Jibia, kuma sun tilasta wa motocin da ke bin hanyar tsayawa.
“Lamarin ya faru ne a ranar kasuwar mako-mako ta Jibia wanda yawanci kan sanya titin ya kasance cikin sintirin ababen hawa.
“‘Yan bindigar sun kuma tilasta wa fasinjoji da dama da ke cikin motocin bin su cikin daji,” in ji shi.
Majiyar wadda ta bayyana cewa titin Katsina zuwa Jibia yana da akalla shingayen tsaro 20 da suka hada da na hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) da kuma na ‘yan sanda, inda ta yi mamakin dalilin da ya sa ba su yi wani abu ba don hana ‘yan bindigar kaddamar da ta’addanci a kan ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba.
Shugaban karamar hukumar Jibia, Bashir Maitan ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta yi martani ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.