‘Yan ta’adda sun yi barazanar sace tare da kashe shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a cikin wani sabon faifan bidiyo da suka saki.
Makonni kadan bayan harin da aka kai wa ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina, ‘yan ta’adda sun yi barazanar sace shugaban.
- ‘Yan Sanda Sun Kama Wakilin LEADERSHIP Na Zamfara, Sun Hana Beli Ko Ganin Sa
- Yunwa Ba Dimokuradiya Ba Ce
An kai wa ayarin tawagar shugaban kasa hari a kan hanyarsu ta zuwa mahaifar Buhari da ke Daura gabanin Sallah.
Mutane biyu sun samu raunuka a harin, wanda fadar shugaban kasar ta ce an dakile harin.
Harin da aka kai wa ayarin motocin ya faru ne a ranar mayakan ISWAP suka kai hari gidan yarin Kuje da ke Abuja tare da kubutar da fursunoni sama da 800 da suka hada da daukacin ‘yan ta’addan da ake tsare da su.
LEADERSHIP ta ruwaito yadda maharan suka yi murna lokacin da suka saki fursunonin Kuje.
A wani sabon faifan bidiyo da suka saki, ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 60 a cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun yi barazanar sace Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai tare da kashe su.
‘Yan ta’addan sun kuma yi ikirarin cewa za su ruguza kasar nan sannan su kashe sauran fasinjojin da ke hannunsu sannan su sayar da sauran.
An sako wasu fasinjojin ne bayan da aka ce sun biya Naira miliyan 100 kudin fansarsu.
Daya daga cikin ‘yan ta’addan ya yi barazanar cewa idan har gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, to za su mayar da yankin tamkar mahauta.
“Wannan shi ne sakonmu ga gwamnatin Nijeriya kuma kamar yadda kuka ga wadannan mutane nan, da yardar Allah za ku ga shugabanninku; Sanatoci da gwamnoninku za su zo gabanmu. Wadannan da kuke gani a nan za mu rike wasu a matsayin bayi mu sayar da su kamar yadda Imaminmu ya fada muku a baya,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa a cikin harshen Hausa: “Kamar yadda ’yan matan Chibok da aka sayar, za mu sayar da wadannan a matsayin bayi. Idan ba ku biya mana bukatunmu ba, za mu kashe wadanda muke bukata mu sayar da sauran. Da yardar Allah, El-Rufai, Buhari, za mu kawo ku nan.”