Rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna ta ce jami’anta na Operation Restore Peace a yankin Galadimawa, sun tarwatsa wani sansanin masu garkuwa da mutane da ke dajin Galadimawa a Jihar, inda suka cafke wani matashim dan bindiga dauke da muggan makamai.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Muhammed Jalige, ya fitar, ya ce an tafka sun arangama da ‘yan ta’addan, inda daga karshe suka mika wuya.
Ya ce ‘yansandan sun yi nasarar cafke daya daga cikin ‘yan bindigar mai suna Yusuf Monore mai shekaru 20 dauke da bindigogi kirar AK47 da AK49, da harsasai kirar dango 7.62 X 39mm da wayar hannu guda uku da kuma tocila.
Ya kara da cewa ana binciken wanda ake zargin saboda har yanzu jami’an na ci gaba da zakulo masu laifin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa, Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, CP Yekini Ayoku, yayin da yake yaba wa irin rawar da jami’an da suka gudanar da aikin, ya ba da tabbacin hada gwiwa tsakanin jami’an tsaro a jihar.
Ya jaddada cewa ‘yan sanda sun jajirce tare da mai da hankali wajen kawar da makiya tsaron kasa baki daya.
Ya kara da cewa, Kwamishinan ya kuma bukaci ‘yan kasa da mazauna jihar da su kasance masu kiyaye doka da oda da kuma gaggauta kai rahoton duk wani mutum da ake zargi ga jami’an tsaro, tare da ba su tabbacin sirrin duk wata hanyar samun bayanai.