Mai Shari’a Inyang Ekwo na babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ya tabbatar da Oladipupo Adebutu a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na gwamnan Jihar Ogun a karkashin jam’iyyar PDP.
Alkalin bayan da ya kori karar da Jimi Lawal ya shigar bisa gasa gabatar da kwararan shaidu da hujjoji gami da kasa tabbatar da abubuwan da ya ke zargi.
Lawal, wanda ya nemi tikitin tsayawa takarar Gwamna na jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar 25 ga watan Mayu, ya kalubalanci nasarar da Adebutu ya samu, yana mai zargin cewa an yi amfani da haramtattun wakilan jam’iyya (delegates) wajen gudanar da zaben fitar da gwanin.
Lawal dai ya yi fatan da rokon cewa kotun za ta soke zaben tare da umartar a sake gudanar da sabon zabe tare da sahihan wakilai (delegates).
A hukuncin na Mai Shari’a Ekwo ya misalta Lawal a matsayin “Mai barna’ da ya shiga cikin jam’iyyar PDP a watan Maris daga jam’iyyar APC kuma ya shiga takarar neman tikitin gwamna na jam’iyyar da aka gudanar a watan Mayu.
Kotun ta ce, Wakilai (delegates) da Lawal ya jero da ke kalubalanta, suna daga cikin jerin wadanda PDP da INEC suka amince wajen gudanar da zabukan fitar da gwani wanda ta hakan ne kuma Adebutu ya samu nasarar zama dan takarar jam’iyyar.