Shugaban ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (AYCF), Alhaji Yerima Shettima ya bayar da tabbacin cewa sai da hadin kai da jajircewa mulkin dimokuradiyya zai tabbata a Nijeriya.
Shugaban ya bayyana haka ne a wani taron gangami domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai wanda ya gudana a jihar Kaduna.
- NNPCL Ya Ƙulla Sabuwar Yarjejeniya Ta Samar Da Ɗanyen Mai Na Shekaru Biyu Da Matatar Dangote
- Ci Gaban Sin Mai Inganci Ya Samar Da Damammaki Ga Duniya
Yerima Shettima, wanda yana daga cikin masu neman takarar kujerar Dan majalisar dattawa daga tsakiyar jihar Kaduna, ya kara da cewa, lokaci ya yi da al’ummar kasar nan za su rungumi zaman lafiya da hadin kai domin ganin kasar ta ci gaba ta bangarori da dama.
“Ina kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kai a gidajenmu, al’ummominmu, da fadin ƙasarmu. Tare, cikin haɗin kai da ƙauna, za mu iya gina Nijeriya ta mafarkinmu. Barka da ranar ‘Yancin Kai!” in ni Shettima.
Akan hakan, Shettima ya jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wanda ya samar da abubuwan ci gaban ƙasa, inda ya ƙara da cewa, idan aka ƙara haƙuri abubuwa za su yi kyau a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp