Shugaban Hukumar Tace Fina-finai na Jihar Kano, Abba El Mustapha yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARTB ya bayyana cewa, tun bayan zamansa shugaban wannan hukuma ta dab’i da adabi ta jihar Kano, akwai korafe-korafe da dama da yake samu daga mutane.
El Mustapha ya kara da cewar a wani lokacin hatta sallah sai ya yi da gaske yake samu ya yi domin mutane da yawa ne ke zuwa suna kawo korafe-korafensu a kan abubuwa daban-daban.
- Ina Fatan Fim Ya Yi Sanadiyyar Shiga Ta Gidan Aljanna – Sadiq Sani Sadiq
- Abba Gida-Gida Ya Nada Sunusi Oscar A Matsayin Mataimakinsa Akan Masana’antar Kannywood.
Tun lokacin da na zama shugaban wannan hukuma, na dauki matakai da dama domin saita al’amura,hakan ya sa na kirkiro wasu dokoki da suka hada da sabunta rajista ga kowane dan fim a masana’antar Kannywood.
Na kuma bullo da shirin hana tallace-tallace marasa ma’ana da ke bata tarbiyar yaranmu, sannan na bullo da maganar cewar duka masu sana’ar downloading su tabbatar da sun sayi foster kafin su tura wa kwastomominsu fina-finai.
Wannan matakai da na dauka yasa mutane suka gane cewar da gaske muke yi a kan alkawarin da muka dauka wajen gyaran wannan hukuma ta ‘Kano Censorship Board’ da mai girma gwamna ya damka muna amanarta.
Dalilin wannan ya sa mutane suke kawo mana kukansu a kan duk wani da suka gani ya dauko hanyar bata tarbiyar yara da sauran laifuka makamantansu da suka shafi aikinmu na dab’i da adabi domin mu taka masa burki.