Masu iya magana dai sun ce sarki goma zamani goma. Rantsar da shi ke da wuya sai sabon shugaban Amerika, Donald Trump ya fara fitar da wasu manufofi na rashin mutunci tsakaninsa da sauran kasashen duniya. Kama daga korar bakin haure, ficewa daga cikin wasu kungiyoyi na kasa da kasa, ya zuwa ga batun cinikayya tsakanin Amerika da sauran kasashen duniya.
Mataki na baya bayan nan dai wanda ya baiwa kowa mamaki da takaici shi ne kara sanya haraji kan ma’adanan karafa da Sanholo da ake shigar da su Amerika. Wannan mataki dai ya janyo Allah wadai daga abokan cinikayya da Amerika a fannin Tama da Sanholo, da suka hada da kasashen kungiyar tayayyar Turai, Canada da kuma Mexico, wadanda kuma suka lashi takobin daukar matakan ramuwar gayya kan wannan karin haraji.
- Kasar Sin: Yankin Asiya Da Tekun Pasifik Ba Wajen Kartar Kasashe Masu Karfin Iko Ba Ne
- EFCC Ta Cika Hannu Da Mutane 15 Kan Zargin Zamba Ta Intanet A Abuja
Ranar 4 ga watan Maris ne ake sa ran wannan dokar karin haraji da Mr. Trump ya rattabawa hannu za ta fara aiki, inda kuma ya kara da cewa babu wata kasar da za a cirewa hula. Ko da yake ya ce mai yiyuwa ne a dan sassautawa Australia saboda gibin kasuwanci da take fuskanta.
Idan ba’a manta ba, a zamanin shugabancinsa a shekara ta 2018, Mr. Trump ya taba kara haraji kan Tama da kashi 25, ya kara harajin Sanholo zuwa kashi 10 da ake shiga da su daga Canada da Mexico da kuma Tayayyar Turai, inda a lokacin Brussels, hedkwatar tarayyar Turai ta dauki matakan ramuwar gayya ta hanyar kara haraji kan barasa, ruwan lemo da babura da suka fito daga Amerika. Daga bisani bayan shekara daya Trump ya janye wannan karin haraji kan Canada da Mexico. Yayin da sai shekara ta 2021 aka janye karin a kan kasashen kungiyar tayayyar Turai.
Wannan sa in sa da ake yi tsakanin Amerika da kasashen dake huldar kasuwanci da ita ba zai haifarwa Amerika da mai ido ba. Domin kuwa idan aka yi nazari a tsanake, za a ga cewa illar da wannan mataki zai haifar ga tattalin arzikin Amerika mai tarin yawa ne. Na farko dai masana’antun da suka dogara da wadannan ma’adinai na karafa da Sanholo za su fuskanci hauhawar farashi, abin da zai rubanya yawan kudaden da suke kashewa wajen sarrafa wadannan ma’adanai, hakan kuwa zai tilasta masu rage yawan kayan da suke kerawa sannan kuma su rage yawan ma’aikata.
Abin ban takaicin shi ne duk wannan hauhawar farashi da karin harajin zai haifar a kan talakawa zai kare, domin kuwa farashin kayayyakin da ake kerawa daga irin wadannan ma’adanai na Karafa da Sanholo zai yi tashin gwauron zabo.
A bayyane take cewa kasashen da wannan karin haraji ya shafa ba za su rungume hannuwansu ba su sanya ido Amerika ta ci karenta ba babbaka, babu shakka su ma za su dauki matakan ramuwar gayya, ta hanyar kakaba haraji a kan kayayyakin da Amerika ke fitarwa. Wannan lamari zai haifar da yakin ta fannin kasuwanci, abin da ba zai amfanawa kowa ba.