A kokarin lalibowa da nemo mafita ta karshe kan rikicin da ke faruwa a cikin jam’iyyar PDP, mambobin Majalisar amintattu na jam’iyyar sun gana da gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, a gidan gwamnati da ke Fatakwal a ranar Talata.
Da yake magana bayan kammala ganawar sirri da suka yi tare da gwamnan, mai rikon mukamin Shugaban Majalisar amintattu na jam’iyyar kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Adolphus Wabara, ya ce, ganawar ta gudana cikin kwankiyar hankali amma dai ba kammalata ba tukunna, inda ya ayyana ta a matsayin ‘Inkunkulusib’.
Wabara ya ce: “Mun kwashe sama da awanni hudu muna tattaunawa da hazikin gwamna na jihar Ribas. Mun shafe sama da awa hudu amma ba a kammala ganawar ba.
“Kun san tabbatar da zaman lafiya na iya daukan lokaci. Amma, Ina tunanin mun kusa cimma gaci. Mun na da kwarin guiwa. Mun ji bangaren gwamnan. Za mu koma Abuja mu hado duk abubuwan da muka tattaro.
“Ganawarmu ta yi armashi, amma wani abu guda da nake son kowa ya sani shine wannan ahlin za ta ci gaba da zama gida daya a lema daya wato PDP, kuma da izinin Allah za mu kai ga kammalawa cikin nasara. Tare da hadin kai shi (Wike) da sauran dukkanin Gwamnoni za mu kai mataki na gaba.”
Ya nuna kwarin guiwarsa na cewa nan kusa kadan za su shawo kan matsalolin tare da tabbatar da cewa PDP ta Kara zama a karkashin lema daya domin tunkarar abubuwan da suke gabanta.
Ya kara da cewa a daidai lokacin da gangamin yakin neman zaben na shugaba kasa ya kankama, jam’iyyar za ta tabbatar dukkanin abubuwan da suka kamata suna layin da ya dace domin kai jam’iyyar ga nasara.
Da yake ganawa da ‘yan jarida, gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya ce, abu mai matukar muhimmanci shine PDP tana dinke wuri guda.