Da Yaya Mace Ta Ke Ba Wa Namiji Shawara?

Mafiya yawan mata sun debe haso da cewa mazansu za su taba karbar shawararsu. A iyakar saninsu, maza sam ba sa karbar shawara daga matansu. Balle kuma su yarda da gyara. Sai dai abin da yawancin matan ba su sani ba shi ne, akwai hanyoyin da su ka fi dacewa a bi yayin da ake son yi wa maza gyara ko a ba  su shawara su karba.

Bana mantawa, a bara, mun taba tattauna wasu daga dabi’un maza da wasu mata. Daga korafin da su ka fi yi game da maza a lokacin shi ne “Su maza gani suke yi komai sun iya. Sam ba sa daukar shawara, kuma ba sa karbar gyara. Wai mutum ba zai yi kuskure ka ce masa ya gayara  ba. Ba zai sa kayan da ba su dace ba a ce ya sauya, sai abu ya zama tashin hankali!”

Abin da mata su ka kasa ganewa game da namiji shi ne, a daidai lokacin da yake aikata wani abu ba daidai ba, sam ba ya son wai matarsa ta zauna tana yi wasa wata doguwar lakca. Hanyar da ta fi dacewa ta bi ita ce, ta nuna masa ta karbe shi a haka. Ina nufin ta kau da kai, ta ki nuna masa abin da yake yi ba daidai ba ne. kuma ta ki nuna kyama ko fushi da shi bi sa ga wannan abin, tare da cewa ya san ta sani. To a irin wannan lokaci, da kansa zai iya bijiro mata da maganar. Watakila kai tsaye ya so jin ra’ayi ko shawararta. A irin wannan lokaci ne kuma za ta iya gabatar da shawarwarinta ba tare da ya harzika ba. Amma yana da kyau mata su sani cewa, maza suna bukatar su sami karbuwa da cikakkiyar kwanciyar hankali daga matansu kafin su bude musu ciki su tattauna damuwarsu da su, su kuma nemi shawara.

A hannu guda kuma, idan mijinki ya kasance ba mai tattaunawa da ke ba ne in kin bi ta wannan siga. To za ki iya tunkararsa da magana game da abin da kike son gyara ko shawarar da kike son ba shi. Amma fa ta hanyoyi na azanci. Ga guda hudu daga irin wadannan hanyoyi:

  1. Mace idan ba ta son wasu kaya da mijinta yake sawa, watakila ba sa yi masa kyau. Ba wai dogon bayani da yake bayyana rashin dacewar kayan da shi ya kamata ta yi ba. Za ta iya cewa cikin sauki: “Ni kuwa ba na son wannan rigar. Sai in ga kamar rage maka kyau take. Ina fatan dai da yamma za ka sauya wata.” Ba lallai ne ya cire ta a wannan lokacin ba. Amma sakon tabbas yana shiga zuciyarsa, kuma zai fara tsanar ta shi ma. Asalin al’amari shi ne, kowane namii yana son burge matarsa. In kuma ki ka ga alamun ya yi fushi, kamar bai ji dadin maganar ba. Ki ba shi hakuri, musammam “Ka yi hakuri, ba ina nufin na fi ka sanin kayan da su ka dace ka sa ba ne.”
  2. Ko kuma kai tsaye idan hadin da ya yi ne ba su dace ba, ki ce da shi. “Kar fa ka manta bulun kaya ka saka. Amma shi ne za ka sa jar hula? Wannan hadin ni dai ba na ganin kyansa. Me zai hana ka gwada bakar hularka?”
  3. Haka nan, za ki iya cewa da shi, a daidai lokacin da ya sa wadannan kayan. “Don Allah ko za ka yarda in raka ka kasuwa ranar da za ka sayi sabbin kaya nan gaba? Ka ba ni dama ka ga yadda zan zabo maka kayan da za su dace da jikinka sosai.?” Idan ki ka ga ya yi dariya, alama ce ta cewa za ki iya bayyana masa rashin dacewar kayan da ya sa a halin yanzu. Amma idan ki ka ga ya murtuke, to alama ce ta cewa shi ba ya bukatar irin wannan kulawar a wannan lokacin. Sai ki rabu da shi, ya je. Haka nan, idan ma kin ga sakin fuskar kar ki manta, kar ki yawaita magana. Yi bayanin  cikin takaitattun kalmomi. Daya daga manyan matsalolin da suke sawa maza su kasa ba wa mata cikakkiyar damar magana a lokacin da za su fita, ko suke da ayyuka da yawa shi ne, mata ba su iya takaita  zance ba. Abin da za a bayyana a cikin kalmomi biyar, sai su zamar da shi na kalmomi goma sha biyar ko ma ashirin.
  4. Ko idan kin san mai saurin fushi ko mai yawan nuna isa ne, ta ce. “Akwai abin da nake son in fada maka, amma na rasa ta yadda zan yi maka maganar. Ina tsoron kar in fada in yi laifi. Ko za ka dan saurare ni ka ji abin da yake raina, in ya so sai ka ba ni shawarar yadda ya kamata in bayyana shi?” Wannan shi zai sa ya shirya wa karbar kalubale a zuciyarsa. Wato ya fara kaddarawa cewa za ki yi masa wata magana wadda ba lallai ne ta yi daidai da ra’ayinsa ba. Wannan masaniya da yake da ita cewa yanzu za ki kalubalance shi, ita ce za ta rage masa girman zafin maganar ko kuma ma ta dauke masa gaba daya. Maimakon kawai ya ji ta katsam ba tsammani, ya tunzura.

Bari mu dubi wani bangare da mata suke yawan ganin baiken mazajensu, da kuma son yi musu gyara. Wato bangaren cin abinci. Misali an kawo masa abinci da nama da cokula da wuka, shi kuma ya fi jin dadin ya dauki namansa da hannu ya rika yaga. Ke kuma kina ganin ai wannan bai dace ba. Abu na farko dole yanayin kallon da za ki yi masa a lokacin ya kasance ba kallo ne na ganin baike ba. Sannan ki ce. “Ko za ka yi amfani da wuka da cokulan?” Amma idan a gaban mutane ne, kar ma ki yi masa magana. Daga baya kya fada masa. “Ina ganin zai fi kyau ka rika cin naman nan da wuka da cokali. Sam ba na jin dadi in na ga kana cin abinci da hannun nan a gaban mutane.”

Haka idan a cikin wata halayya da ba kya so ki ka gan shi, ba za ki yi kamar so kike ki koya masa yadda  zai yi mu’amula ba. Misali idan yanayin yadda yake magana a cikin mutane ne ba kya so, ya fi kyau ki fadi wani abu kamar. “Ban ji dadin yadda kai ma ka dage ka na daga murya haka a cikin mutane ba jiya. Mutane suna ganin kimarka, na tabbata da yawa ba za su ji dadi ba in su ka gan ka kana irin wannan halayya.” Idan kin ga alamar ya ji haushi, ki ba shi hakuri. Amma tabbas maganar za ta yi tasiri nan gaba. Domin ko da ba a garinsu ya ke ba in ya kara takarkarewa zai yi irin wancan ihun sai ya tuno ki. Kuma sai ya sassauta.

Ya na da kyau mata su gane cewa rikon maza tamkar rikon tangaran yake. Tabbas idan kin yi ganganci da shi zai subuce ya fashe. Amma fa idan kin iya ririta shi, to hatta wanke-wankensa abin nishadi ne.

Exit mobile version