Aiki da karatu a gida wani al’amari ne mai ban sha’awa wanda mutum shi ke zaba wa kansa yadda ya dace ya tafiyar da al’amarin, idan ba a manta ba lokacin da annobar cutar Korona ta kunno kai, da irin hakan ne wasu da yawa suka yi karatu a gida. Shi ya sa yanzu abin ya rage wa matasa da ke sha’awar amfani da irin wannan hanyar, su tsara yadda za su yi karatu da hanyoyin da suka kamata ba tare da bata lokaci ba. Wadannan hanyoyin za su taimaka wa duk wanda ke son karatu a gida ya san yadda zai tsara yin shi. A wannan makon za mu fara tattaunawa a kan dabara na 1.
1. Ka tsara abubuwan da za ka yi a ranar da zaka fara yin karatun, ga yadda zaka fi jin dadin tsarin naka da dare kafin ka yi barci. Tsare- tsaren karatu a gida na nuna maka kai kake da damar zabarwa kanka yadda kake son tafiyar da al’amarin ka musamman ma na karatun,sai ka tabbatar da duk abubuwan da za ka yi a ranar, sannan ka duba wanne lokaci ne za ka fi fuskantar matsaloli, da kuma wanne lokaci ne ba zaka hadu da irin hakan ba,idan har ka yi hakan zaka fi samun lokacin da ya fi dacewa da kai.
- Koya Wa Yara Shigar Mutunci (I)
- Iyaye Mu Kara Himmar Samar Da Al’umma Mai Tarin Ilimi –Matar Gwamnan Katsina
Ka zabi lokacin da ya fi dacewa ka yi karatu ko yin bincike hakanan ma kana iya amfani da lokacin da kake kokarin yin hadda ka yi karatu.
Abu mafi dacewa lokacin karatu da hadda shine da sassafe kafin iyali su tashi saboda a lokacin kai kadai ne ba abinda ke damunka,irin wannan lokacin ne zaka fi mai da hankali akan abinda ka ke yi.
Sai dai kada ka manta ka rubuta abubuwan da za ka yi ka rika dan bata lokaci,kana iya raba abubuwan da zaka yi da kuma lokacin,ka sa lokacin cin da za ka ci abinci,wanka,lokacin hutu kai harma da na barci.
Kada ka manta da abubuwan da ka iya kawo maka matsala duk da haka ga han yoyon karatu a gida za ka iya yi ko wanne irin hali ka samu kanka.
Da farko ya dace ka gane wacce hanya za ka iya samun matsalar da zarar ka gane zaka iya sanin yadda zaka iya bullowa al’amarin,idan haka ne cigaba da abinda ka yi niyya idan kuma ba haka bane sai ka samu lokacin da zaka dan yi tunani.Da Zarar ka gane abinda ka iya samar maka da matsala kamata ya yi ka dan yi nazari in abin zaka iya maganin shi shikenan,in har ta kasance haka ne sai ka dauki mataki na gaba idan al’amarin ya gagara sai ka samu ‘yar hutawa ta lokaci ba mai yawa ba.
Idan ka ga matsalar ba zata barka ka yi karatun bas ai ka mai da hankalin ka wajen maimaita wanda ka dade da yi domin kuwa irin wannan bai bukatar ba shi lokaci kamar in da ace sabo ne.
Tunda makarantar da kake /ko kwaleji da kuke tana tsara lokacin da Malamai za su koyar a azuzuwa,lokacin yin ayyukan da suka bada,da dai sauran abubuwa,don haka akwai bukatar kai ma a gida ka tsara lokacin da za ka rika tashi ka wartsake kanka daga barci,lokacin abinci da sauransu,abu mafi dacewa shi ne abi al’amari kamar yadda aka tsara tafiyar da shi.
Daukar ma rai sai an cimma wani buri wannan ma na da matukar muhimmanci domin kuwa babu wanda zai zo daga Makarantarku ya ga ya kake tafiyar da al’amuran karatunka.Wadannan hanyoyin na karatu saboda dalibai ‘yan makaranta za su taimakawa kowa a matsayin wata manuniya yadda mutum zai tsara yadda zai yi karatu.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa…