Wani masanin harkokin tattalin arziki a kasar Ghana, Paul Frimpong, ya ce dabarun kasar Sin na yaki da annobar COVID-19, sun bunkasa farfadowar tattalin arzikin duniya ta fannoni da dama.
Paul Frimpong, babban daraktan cibiyar nazari da bayar da shawarwari kan dangantakar Sin da Afrika, dake da mazauni a Ghana, ya bayyana yayin da yake tattaunawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua a baya-bayan nan cewa, soke wasu matakan yaki da annobar COVID-19 da Sin ta yi a baya-bayan nan, ya aike da kyakkyawan sako ga duniya, kuma ya bunkasa kwarin gwiwar masu zuba jari kan kasar ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Ya ce ya yi imanin cewa, yadda kasar Sin ta shiga sabon matakin na kandagarki da dakile annobar COVID-19, zai ingiza kuzari a harkar samar da kayayyaki a duniya da tallafawa matakan da sauran sassan duniya suka dauka na sake gina tattalin arzikin na duniya.
Masanin na kasar Ghana, ya kuma yi watsi da wasu tsokaci da kafafen yada labarai na yammacin duniya ke yadawa game sassauta matakan yaki da annobar da Sin din ta yi, yana mai bayyana su a a matsayin masu nuna fuska biyu a yunkurinsu na bata sunan kasar Sin.
Ya ce sun yi korafin Sin ta ayyana matakin kulle, sun yi ikirarin matakin ya yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin duniya, inda suka zargi kasar Sin da yunkurin dakile farfadowar tattalin arzikin duniya da gangan. Yanzu kasar Sin ta dage dokar, amma suna ci gaba da korafi. (Fa’iza)