Kiwon zomo, guda ne daga cikin hanyoyin da aka runguma a halin yanzu, domin samar da wadataccen nama a Nijeriya.
Har ila yau, wadanda suka rungumi wannan sana’a ta kiwon zomo, na sama wa kawunansu kudaden shiga tare da ayyukan yi a tsakanin al’umma.
- Tsadar Magunguna Na Barazana Ga Rayukan Majinyata A Nijeriya
- Sabon Shirin Talabijin Ya Fara Gano Wasu Hanyoyin Kasuwanci A Nijeriya
Babban abin sha’awa tattare da wannan kiwo na zomo shi ne, ko a dan karamin waje za a iya aiwtar da shi ba tare da wata matsala ba.
Kazalika, naman zomo na dauke da sinadaran ‘protein, calcium da kuma bitamin’, fiye da wanda ake samu a naman sauran dabbobi.
Har wa yau, sinadaran da ke cikin namansa da suka hada da ‘cholesterol, fat da kuma sodium’, ba su kai yawan wadanda ake samu a cikin naman sauran dabbobi ba.
 Sannan namansa na da dadin ci, ga kuma taushi da gardi; wanda wannan dalili ne ya sa tsofaffin mutane suka fi son mu’amala da shi.
Haka zalika, namansa ba shi da wani haramci a tsakanin kafatanin mabiya addinai, sannan kuma ga shi yana da saurin girma a yayin kiwon sa.
Bugu da kari, macen zomo na haihuwar ‘ya’ya daga kan guda biyu har zuwa guda takwas.
Wasu Daga Cikin Manyan Alfanun Kiwon Zomo Don Kasuwanci:
–Â Zomo na da saurin girma a yayin kiwon sa.
– Sannan namansa ya kere wa na sauran dabbobin dadin ci.
– Macen zomo daya na haihuwar daga kimanin ‘ya’ya biyu zuwa takwas a lokaci guda.
– Ana kuma iya kiwata shi a cikin dan karamin waje ba tare da matsala ba.
– Haka zalika, ba a kashe kudade da yawa wajen kiwonsa, musamman idan aka kwatanta da na sauran manyan dabbobi.
– Har wa yau, namansa na da dadin ci; sannan yana saurin narkewa da kuma saukin taunawa, musamman a tsakanin manya da tsofaffin mutane.
– Kazalika, cin namansa ba shi da wani haramci a tsakanin addinai.
 -Sannan kuma yana daya daga cikin jeren fannin samar da wadataccen nama a tsakanin al’umma.
– Ba kuma a kashe kudin biyan ‘yan kwadago wajen kiwata shi, idan aka kwatanta da sauran dabbobin da ake kiwatawa.
– Wani bangare ne na samar da kudin shiga tare da yyukan yi a tsakanin al’umma.
– Bugu da kari, za ka iya wadatadar da iyalinka da naman zomo ta hanyar kiwata shi.
Dabarun Kiwon Zomo Don Kasuwanci:
Ana samun nau’ikan zomo da dama a fadin duniya, wasu daga cikin nau’ikan, sun hada da bakin zomo wulik, wanda ake samo nau’insa a kasashen duniya kamar Kasar Dutch da nau’in farin zomo da ake samo shi daga Kasar New Zealand.
Bugu da kari, akwai kuma nau’in bakin zomo da ake samu daga Kasar New Zealand da nau’in ja, sai kuma nau’in fari da ake samu daga Kasar Belgium.
Daga cikin wadanan nau’ikan zomaye, za ka iya zabar irin kalar wanda kake bukata ka kiwata.
Dabarun Kiwon Zomo:
A nan, za ka iya yin amfani da robar jarka mai zurfi a matsayin dakin kwana na zomo ko kuma ta hanyar yi musu keji, domin kiwata su.
Kazalika, ana bukatar ka ware wa macen zomo wuri daban a cikin keji, shi ma namijin ka ware masa nasa daban, musamman a lokacin wannan kiwo.
Ciyar Da Su Abinci:
Ya danganta da irin abincin da za ka iya ciyar da su tare kuma da irin sinadarin abincin da suke bukata.
Abincin da ake ciyar da manyan zomaye na dauke da sanarin ‘protein’, wanda ya kai daga kashi 17 zuwa kashi 18 cikin 100 da kuma wanda ya ke dauke da sinadarin ‘fiber’ wanda ya kai kalla kashi 14 shi ma cikin 100.
Har ila yau, akwai kuma wanda abincinsu ke dauke da sinadarin ‘minerals’, wanda ke dauke da kashi 7; sai kuma wanda abincin ya ke dauke da sinadarin ‘calorin’ da ya kai kilo 2,700.
Haka zalika, zomo ya fi cin tsanwan ganye; sannan kuma yana cin alayyahu da karas da kokumba da sauran makamantansu.
Amma, idan har za ka yi kiwon zomo don kasuwanci, yana da kyau ka rika ciyar da su ainahin abincin kiwon kajin gidan gona tare da samar musu da tsaftattacen ruwan sha.