1 Saniya:
Ana bukatar wanda zai kiwata shanu ya tabbatar ya killace inda zai kiwata su da shingen waya, don ya kare su daga fita, wannan shi ne tsarin da ake yi na amfani da shi a zamance.
A fannin kiwon shanu za ka iya samun riba mai yawa, musasaman ganin cewa, ana kara samun bukatar naman shanu da kuma madarar shanun a fadin kasar nan.
- Amfanin Manhajar XENDER A Wayoyin Hannu
- Gwamnatin Bauchi Ta Amince Da Sabuwar Dokar Kafa Kungiyar ‘Yan Sintiri A Fadin Jihar
Haka kuma, ana kara samun bukatar naman shanu a kasashe kamar su, Amurka da Kanada, ganin yadda wadannan kasashen ke kiwata shanu masu yawa.
2 Kaji:
Kiwon kaji, a nan ma’ana samun riba mai yawa, domin ta hanyar sayar da naman Kaji za ka iya samun riba, haka ta hanyar kwansu.
Ana yin amafani da kwansu wajen hada abinci domin kwan Kaji, na da dimbin sinadaran da ke gina jikin ‘yan’adam. Haka ta hanyar kashin Kaji, mai kiwata su, zai iya samun kudi.
Har ila yau, ta hanyar sayar da ‘yantsakin Kaji za ka iya samu riba mai yawa.
Ana bukatar wanda zai kiwata Kajin ya tabbatar ya killace su da waya, don kar su dinga fita, wannan ita ce hanya ta zamani ta yin kiwonsu.
3 Awaki:
A kiwon awaki ana samun kudi masu yawa haka za ka iya samun riba ta hanyar sayar da namansu da kuma nononsu.
Ana kara samun karuwar kasuwar hada-hadar awaki, a dukkan fadin duniya, musamman ganin cewa, ana kara samun bukatar naman akuya wanda ya kai kusan kashi 65 daga cikin dari.
Har ila yau, a yankin Arewacin Amurka, kasawar sayar da awaki na kara tumbatsa saboda karin bukatar da ake da ita ta naman na akuya.
Masana sun sanar da cewa, cin naman akuya na kara wa jikin ‘yan’adam lafiya.
Ana bukatar wanda zai fara kiwata akuya, ya tabbatar ya killace inda zai kiwata su da waya don hana su fita zuwa wani waje.
4 Zuma:
Ana samun riba mai yawa a kiwon Zuma, ana bukatar wanda zai kiwonta ya tabbatar da samu wajen da Zumar za ta dinga saka zumar. Kiwata zuma, bai da wani wuya, matukar ka kiyaye sharuddan kiwonta.
Ana kuma kara samun bukatar zuma, kusan a dukkan fadin duniya, ganin cewa, tana da sinadarai da dama da ke kara wa jikin ‘yan’adam lafiya.
Ga wanda zai fara kiwon zuma, ana bukatar ya tabatar da samar da kariya ga gurin da zumar za ta dinga zuba zumar, musamman domin ya kare ta daga harin dabbobin da ke cin kwari.
5 Zomo:
Ga wadanda suka rungumi kiwon zomo za su iya samun amfani mai yawa, musamman ganin cewa, ana kara samun bukatar naman Zomo.
Masana kiwon lafiya sun ce cin naman zomo na kara wa jikin ‘yan’adam lafiya, musaamman ganin cewa, zomo na dauke da sinadarin protein.
Ga masu kiwata zomo, za su iya sayar da ‘ya’yansu don su samu kudi, haka ana yin amfani da kashinsu wajen takin gargajiya da ake zuba wa a gonakai.
Ana bukatar wanda zai kiwata zomo, ya tabbatar da ya killace inda zai kiwata su da waya don ya hana su fita zuwa wani waje ko kuma kare su daga dabbobin da za su iya kashe su ko kuma yi musu illa.