Dabi’u wadansu halaye ne ko yadda mutum yake tafiyar da rayuwar sa wannan kuma abin ya shafi ko dai bi hanyoyin da suka kamata, ko kuma abin ya kasance akasin haka, wanda idan ba sa’a aka yi ba sai an kai ga cewar Allah karre gaba.
Su wadannan dabi’un sun hada da farko ya kasace mutumin da yake baya da kama kai, duk abinda yaga dama sai ya aikata shi bai san ko ya manta cewae ya fa girma.Ya kasance ya rika rayuwa wadda bata kamace shi ba alal misali ace bayan ya ci zamaninsa ya kuma cesai yayi nba wasu.
mai karamar magana duk maganar daya fada daga karshe sai abin ya zama an gano cewar babu kamshin gaskiya,abinda ya fada da baki daban wanda ke zuciyarsa kuma daban.
Kasancewa Magulmaci wato ya zama mai maganar data shafi gulma,duk wata maganar wani ko wasu a wannan unguwar ko kuma cikin garin,to shine wanda zai fara bayyana ta, da zarar ya ga wani mutum shi ne zai fara ce masa, “Ai wane kuma shi tashi ta kare, ka kuwa ji abubuwan da ya yi” kai da dai sauran maganganun da basu dace ba.
Bugu da kari kuma shi da makwabtansa babiu zaman lafiya, bai bar wadanda suke unguwa daya ko gari daya, duk ta inda aka bullo ma shi,bai son zaman lafiya shi dai farin cikinsa ya ga na tufke da fada ko wanne lokaci ga shi nan dai babu kama kai, duk abinda ya ga dama shi zai furta ba tare da tunanin me da me za su iya biyo baya.
Daga karshe kuma abin ya kan kasance duk garin ko unguwar ya kasance ba maganar da ake yi sai tasa, wato ta rashin jin dadin zama da shi, ba domin komai ba sai saboda dabi’unsa.