Shafi ne da ya saba zakulo muku manyan jarumai har ma da kanana, daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wani bakon na musamman, wanda ya shafe tsahon shekaru ashirin da biyar a cikin masana’antar Kannywood wato, KAMALU MIJINYAWA. Inda ya bayyanawa masu karatu irin gwagwarmayar da sha kafin shiga cikin masana’antar, har ma da wasu batutuwan da suka shafi rayuwarsa.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA Kamar haka.
Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanka, tare da sunan da aka fi saninka da shi.
Kamalu Mijinyawa shi ne sunan da kowa ya sanni da shi, kuma shi ne cikakken sunana.
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
An haife ni a unguwar Tudun Nufawa dake Kano Municipal, na yi karatun firamare a jakara ‘Special Pramary School’, na yi sakandare a Gwammmaja 2. Sannan babban Sakandare a ‘GSS Dala’. Na yi karatun ‘Diploma’ a fannin ‘computer’, sannan na yi ‘National Diploma’ akan lafiyar hakori ‘Dental Surgery Technician’.
Ya batun iyali, shin akwai ko babu?
Ina da Aure, mata ta daya da ‘ya’ya biyar biyu maza uku mata.
Wane rawa ka ke takawa a cikin masana’antar Kannywood?
Na farko zan iya cewa ni ‘film maker’ ne, amma nafi karfi a ‘directing’. Sannan ina ‘Camera’ ina rubutu, Ina ‘acting’, Ina ‘Editing’.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Tun daga kallon indiya ‘da’ da ake yi Asabar da Lahadi, sannan na kasance ina san kallon irin fina-finan ‘cartoon’ a lokacin muna makarantar sakandare a shekarun baya wajan 1996, mai suna Bakandamiyar Rikicin Duniya’. Ana yin wasu fim din hausa wadanda suka fara jan hankalina wajan tunanin ina da abin da zan iya a harkar fim. Akwai wani yayana wanda muke yin komai tare mai suna Hassan Mijinyawa, muka yi shawara akan yadda za mu kirkiri wani fim da za mu yi. Muna cikin shirye-shirye mu akwai wani daya daga cikin dan’uwan mu ya yi karatun da ya shafi fim, aikin jarida yana ba mu karfin gwiwa sai Allah ya karbe shi wato ya rasu a shekara 1998 mai suna Yusif Mijinyawa. Sai muka yi shiru zuwa wani lokaci, kafin 2000 muka dawo da karfin mu inda muka fara yin aikin fim ka’in da na’in.
Za ka yi kamar shekara nawa da fara harkar fim?
A kallla shekara ashirin da biyar.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Maganar kantawaye ni dai ban santa ba, dan ba a yi min ba.
Ya batun iyaye lokacin da za ka sanar musu kana sha’awar shiga harkar fim, ko akwai wani kalubale da ka fuskanta daga gare su?
Gaskiya ni dai ban samu wata matsala ba sai dai kawai nasihohi da kuma lallai mutun ya kula da kansa da addini sa kada kayi wani abu da zai keta ma mutumci sun bani goyan baya dari bisa dari.
Mu dan koma baya kadan, cikin abubuwan da ka lissafo wanda kake taka rawa cikin masana’antar, da wane bangare ka fara?
Daraktin, kuma har yanzu shi ne wanda na fi so.
Kafin ka fara daraktin, shin ka koya ne a wajen wani, ko kuwa ka shiga masana’antar ne da iyawarka?
E, gaskiya farkon shiga ta ganin yadda ake yi nayi na fara, amma daga baya na je sani online da ‘workshop’ da wasu karatuttuka da suka shafi harkar fim.
Ya farkon fara daraktin dinka ya kasance?
E, gaskiya ban sami wani kalubale ba, saboda wadanda na fara aiki da su sun bani hadin kai, sosai duk da cewa duk inda ka fara dole akwai ‘yan masaloli da na fuskanta wajan rashin sabo. Ace ni ne nake daraktin wasu manyan jarumai akwai abinda ya taimakamin a lokacin na dau kwararrun ma’aikata.
A wane fim ka fara daraktin, kuma ya karbuwar fim din ya kasance, ga masu kallo?
Akwai wani fim na kamfani na mai suna ALLURA shi ne na fara daraktin, kuma a lokacin ya samu karuwa domin muna siyar da ‘right’ na CD tun daga siyarwa masu buga wannan CD aka maida kudi aka ci riba, ya karbu sosai a wajan mutane.
Wane abu ne ya fi baka wahala a bangaren daraktin?
To abinda yake bani wahala ko kuma haushi shene jarumina yaki yin abinda aka sashi wannan yana sani inji aikin ya fita daga raina
Za mu cigaba mako me zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp