A ranar 14 ga wata bisa agogon wurin, gwamnatin Amurka ta sanar da kara kakaba haraji a kan wasu kayayyaki daga kasar Sin da kudinsu ya kai dalar Amurka kimanin biliyan 18, kafin daga bisani shugaban kasar ta Amurka Joe Biden ya rubuta ta kafar sada zumunta cewa, “dazun nan na sanar da kakaba jerin sabbin haraji a kan kayayyakin da ake shigar da su daga kasar Sin, kaso 15% a kan karafa da Saholami da kaso 100% a kan motoci masu amfani da lantarki, sai kuma kaso 50% a kan farantan samar da lantarki ta hasken rana. Kasar Sin na da niyyar jagorantar sana’o’i masu alaka, ni kuma ina da niyyar tabbatar da fifikon Amurka a fannonin.”
Abin dariya shi ne, a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2019, shugaba Biden din da kan sa ya rubuta ta kafar sada zumunta cewa, “Trump ba shi da masaniya, yana ganin kasar Sin za ta biya harajin da ya buga, amma kowane dalibi da ya fara karanta ilmin tattalin arziki zai iya tabbatar da cewa, jama’ar kasar Amurka ne suke biya. Ko mai karbar kudin kaya a kantin sayar da kayayyakin masarufi na “Target” ya san me ke faruwa, sun fi Trump sanin tattalin arziki.”
- Matakin Amurka Na Kara Buga Harajin Kwastam Kan Hajojin Sin Babban Kurkure Ne
- Xi Ya Yi Kira Da A Karfafa Azamar Yayatawa Da Kare Babbar Ganuwar Kasar Sin
Shin ko Mr. Biden shi ma ya rasa ilminsa na tattalin arziki bayan da ya hau kujerar shugaban kasar Amurka? A’a, ba haka ba ne, yana da cikakkiyar masaniya a kan me harajin da ya kakaba zai haifar ga kamfanonin kasar da ma al’ummarta. Bisa kididdigar da kamfanin Moody ya yi, masu sayayya na kasar Amurka suna biyan kaso 92% na harajin da gwamnatin kasarsu ta sanya wa kayayyakin kasar Sin, abin da ya sa duk wani magidancin kasar ke biyan karin dala 1300 a kowace shekara. Wani sharhin da jaridar Wallstreet Journal ta fitar a ranar 14, ya yi nuni da cewa, matakin da gwamnatin Amurka ta dauka tabbas zai gurgunta tsarin samar da kayayyaki ga kamfanonin kasar Amurka, wanda hakan zai kara kudin da masu sayayya da ma kamfanoni na kasar suke biya.
Amma me ya faru ga shugaba Biden har ya sauya matsayinsa a kan batun haraji a kan kayayyakin kasar Sin. Lallai bana ne za a gudanar da babban zabe a kasar Amurka, amma tattalin arzikin kasar na fama da matsalolin da suka hada da hauhawar farashin kaya, da babban gibin kudi da sauransu, don haka ma gwamnatin kasar kamar yadda ta saba yi, take kokarin karkata hankalin al’ummarta ga kasashen ketare. Yadda gwamnatin Biden ta dauki wannan mataki a daidai wannan lokaci, manufa ce ta siyasa, ta bayyana tsattsauran matsayinta a kan kasar Sin, don neman samun karin kuri’u a wasu jihohi marasa tabbaci.
A ganin Clark Packard, masani a cibiyar nazari ta Cato ta kasar Amurka, sabon matakin haraji da gwamnatin Biden ta dauka, ya sake dora burin siyasa da yake neman cimmawa a kan muradun kasar baki daya. A zahiri dai, idan an kwatanta da abin da yake neman cimmawa ta fannin siyasa, moriyar kasa da ta jama’a sam ba su da daraja, ballantana ma batun ingancin tsarin samar da kayayyaki na duniya, da farfadowar tattalin arzikin duniya, da‘yancin ciniki, da ma kokarin da kasa da kasa ke yi na tinkarar sauyin yanayi.
Duk da haka, daukar matakan da ba su dace ba na dakile kamfanonin wasu kasashe, ba kawai zai lalata moriyar kamfanoni da masu sayayya na kasar ba ne, har ma zai lalata bunkasuwar masana’antu masu nasaba na kasar ita kan ta. Yadda ‘yan siyasar kasar suke iya kokarin cin babban zabe, amma suna zubar da kimar kasar a idon duniya, kuma zai haifar musu da karin matsaloli a cikin gida. (Mai Zane:Mustapha Bulama)