Watannin da suka shafe ana wasan ɓuya sun ƙare domin dai tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, zai gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja gobe Alhamis.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, za ta gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin cin hanci da rashawa.
- Yau Za A Yi Mugun Zafi Mai Haɗari A Abuja, Sakkwato, Kano Da Kogi, In Ji NiMet
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2 Daga Daliban Da Suka Sace A Kogi
Lauyan Yahaya Bello, Abdulwahab Mohammed, ya tabbatar wa kotu a ranar 10 ga watan Mayu cewa wanda yake karewa zai halarci zaman shari’ar, yana mai jaddada cewa Yahaya Bello ya ƙi halarta ne a baya saboda rashin tsaro.
A baya dai mai shari’a Emeka Nwite ya yi watsi da buƙatar dakatar da shari’ar, inda ya ce hukumar EFCC za ta bi ƙa’idojin shari’a tare da tabbatar da cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a kan tabbatar da tsaron rayuwar tsohon gwamnan ba.
Bayyana a kotun ta biyo bayan dagewar da Mai shari’a Nwite ya yi cewa tsohon gwamnan ya mutunta tsarin shari’a.
Alkalin kotun ya jaddada cewa ba shi da laifi har sai an tabbatar da laifinsa a kotu sannan kuma ya tabbatar da cewa ayyukan EFCC za su ci gaba da kasancewa a kan iyakokin doka.