A ranar 25 ga Fabrairun 2021 ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin ta samu cikakkiyar nasarar kawar da fatara. Yayin da aka fitar da mazauna karkara miliyan 98.99 na karshe daga kangin talauci. Wannan gagarumar nasara ba wai kawai ta taimaka wajen cimma muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya ba, har ma da baiwa kasar damar cimma burin farko na ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya na “kawo karshen talauci a duk fadin kasar”, shekaru 10 kafin lokacin da aka tsara.
A shekarar 2021, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta kafa cibiyoyin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka na yin musayar fasahohin aikin gona na zamani, domin inganta zamanantar da aikin gona a nahiyar Afirka. Bayan shekaru uku, wato a wannan shekara ta 2024, shugaba Xi ya kara bayyana cewa, za a aiwatar da ayyukan hadin gwiwa guda 10 a cikin shekaru uku masu zuwa, wadanda suka shafi fannoni daban-daban da suka hada da ilmantar da juna tsakanin al’ummomi, da ci gaban cinikayya, da hadin gwiwar sassan masana’antu, da dai sauransu. Bugu da kari, an karfafa gwiwar cibiyoyi da kamfanoni na kasar Sin da su raya kauyukan gwaji game da ci gaban aikin gona da kawar da fatara a Afirka, tare da tallafawa shirin “Kamfanoni dari a kauyuka dubu” da hadin gwiwar kamfanonin kasar Sin a Afirka suka kaddamar don gudanar da ayyukan kyautata zamantakewar kamfanoni.
- WHO Za Ta Kwashe Mata Da Kananan Yaran Gaza 1,000, Zuwa Turai Don Kula Da Lafiyarsu
- Xi Ya Jaddada Bukatar Ingiza Bude Kofa A Matsayin Koli Domin Cimma Nasarar Sauye Sauye Da Samar Da Ci Gaba
A karkashin shirin rage fatara da bunkasa aikin gona kuwa, kasar Sin ta kaddamar da ayyukan kawar da fatara da kuma ayyukan noma guda 47, wadanda ke ba da taimakon fasaha ga Malawi, Burundi da Cote d’Ivoire. Tare da kusan ma’aikatan noma 9,000 da kwararru a fannin noma 500 da aka aika zuwa Afirka, shirin ya amfanar da kananan manoman Afirka sama da miliyan daya, wanda ya taimaka wa nahiyar wajen samun fasahohin noma na zamani.
A ranar 17 ga Oktoban shekarar 2024 ne aka yi bikin ranar yaki da fatara ta kasar Sin karo na 10, wacce ta zo daidai da ranar kawar da talauci na duniya karo na 32. Tare da samun goyon bayan sama da kashi daya bisa uku na al’ummar duniya da Sin da Afirka ke wakilta, da jajircewa daga gwamnatocinsu, hadin gwiwar Sin da Afirka kan kawar da fatara zai yi tasiri sosai a kokarin da ake yi na kawar da talauci a duniya. (Mohammed Yahaya)