Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMet) ta yi hasashen cewa tsawon kwanaki uku a jere daga Litinin da Talata da Laraba a fadin Nijeriya za a fuskci zazzafar rana tare da giza-gizai a yankin arewaci, inda ake sa ran samun tsawa a wasu sassa na jihar Taraba.
Haka zalika, yankin Arewa ta tsakiya na iya fuskantar washewar sararin samaniya tare da yiyuwar afkuwar tsawa a Binuwai
- Yau Za A Yi Mugun Zafi Mai Haɗari A Abuja, Sakkwato, Kano Da Kogi, In Ji NiMet
- Ƙananan Hukumomin Kano 14 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwan Sama — NiMET
An yi hasashen cewa jihohin kudancin Nijeriya za su iya fuskantar tsawa a yankuna kamar Cross River da Akwa Ibom.
A ranar Talata kuma, NiMet ta yi hasashen yanayin rana tare da gajimare mai hadari a yankin arewa, da yiwuwar tsawa a wasu sassan Adamawa, Kaduna, da Taraba.
Ana sa ran yankin Arewa ta tsakiya zai kasance da gajimare, inda za a iya samun tsawa a jihohi kamar Binuwai da Kogi.
A ranar Laraba kuwa, NiMet ta yi hasashen ci gaba da samun irin wannan yanayin a faɗin Nijeriya. Yankin arewa na iya fuskantar yanayi na rana tare da giza gizai tare da tsawa jifa-jifa a wasu sassan jihohin Taraba da Adamawa da Kaduna.
A yankin Arewa ta tsakiya, ana sa ran samun gajimare da safe, tare da tsawa a wurare kamar Babban Birnin Tarayya Abuja da Filato.
Da ƙarshe, NiMet ta shawarci jama’a da su yi taka tsantsan, musamman a wuraren da ake iya samun faruwa tsawa, saboda iska mai ƙarfi da ruwan sama.
Bugu da ƙari, hukumar ta ba da shawara ga ma’aikatan jiragen sama da su kasance masu neman bayanai akai-akai da hasashen yanayi daga NiMet don tsara ayyukansu yadda ya kamata a tsakanin yanayi daban-daban a fadin Nijeriya.