Yayin da wa’adin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), ta bai wa gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar, ya cika, fitaccen malamin Addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya shiga yaki da kasar da ke makwabtaka da Nijeriya.
Shahararren malamin, wanda shi ne shugaban darikar Tijjaniya a Nijeriya, ya kuma bukaci majalisar dokokin kasar nan da kada ta amince da bukatar da shugaban kasar ya gabatar mata kan yakar Nijar.
- AU, UN Da ECOWAS Sun Garzaya Nijar Don Tattaunawa Da Sojin Juyin Mulki
- Kwatsam Ta Zayyana Ƙa’idoji Kafin Fara Shigo Da Kayayyaki Daga Iyakoki
A cewar dattijon malamin, maimakon su shiga yaki da kasar, kamata ya yi shugaba Tinubu da sauran shugabannin ECOWAS su tattauna da gwamnatin mulkin sojan Nijar da ta hambarar da shugaba Mohammed Bazoum.
Sheikh Bauchi ya bayyana haka ne a Bauchi a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida, inda ya kara da cewa Nijeriya da Jamhuriyar Nijar na da dadaddiyar alakar da ke bukatar kara karfafa ta.
“’Yan Nijeriya da Nijar sun dade a tare. Don haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta tsunduma cikin harkokin diflomasiyya da nufin karfafa kyakkyawar alakar bunkasar tattalin arziki da ci gaban kasashen Afirka ta Yamma,” in ji shi.
A cewar Shehin malamin, ya yi gargadin cewa, “yana da kyau a samar da wani kuduri na aminci don kaucewa zubar da jinin wadanda ba su ji ba ba su gani ba. ”
Daga nan sai ya bukaci sauran shugabannin Afirka ta Yamma da sauran masu ruwa da tsaki da su rungumi tattaunawa ta diflomasiya.
“Muna kira ga Shugaba Tinubu; Muna kuma kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da dukkan shugabannin ECOWAS da masu ruwa da tsaki da kada su shiga da Nijar.
“Wannan kudirin ne na ceto rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da kuma ceto mutane daga shiga cikin kuncin rayuwa,” in ji Sheikh Dahiru Bauchi.