• English
  • Business News
Monday, July 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daidaiton Ƙasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Ci Gaban Ƙasashen Duniya

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Daidaiton Ƙasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Ci Gaban Ƙasashen Duniya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

“Ya kamata a ƙara rungumar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yayin da duniya ta tsunduma cikin rikice-rikice da rashin zaman lafiya,” waɗannan kalaman firaministan ƙasar Sin Li Qiang ne yayin da yake jawabi a wajen buɗe taron shekara-shekara na sabbin jagorori karo na 14, wanda aka fi sani da Davos na lokacin zafi, da ya gudana a ranakun 27 zuwa 29 na Yuni a Tianjin, ƙasar Sin. 

Taron da ya samu mahalarta kusan 1,500 daga fannoni daban daban kama daga ‘yan kasuwa, hukumomin gwamnatoci, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma malaman jami’o’I daga ƙasashen duniya kusan 100, kalaman Li saƙo ne zuwa ga al’ummar duniya da ke fuskantar rashin zaman lafiya da rikice-rikicen siyasa da bambance-bambancen aƙida suka haifar. Dunƙulewar kasuwancin duniya na fuskantar barazanar takunkumi na bai-ɗaya daga wasu ƙasashen yamma. Kana, yunƙurin samun haɗin gwiwar kimiyya ya samu cikas ta hanyar siyasa. Haka kuma yunƙurin yin musayar al’adu ya samu cikas ta rashin yarda, matsin lamba da rikice-rikicen siyasa.

  • Amfanin Juna Shi Ne Tushen Hadin Gwiwar Afirka Da Sin

An amince da ƙasar Sin a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi cin gajiyar dunƙulewar duniya. Wannan gaskiya ne, tun bayan da aka yi gyare-gyare da bude ƙofa ga waje, ƙasar Sin ta samu nasarorin da ba a taba ganin irinta ba a harkokin mulki. Ta kawar da matsanancin talauci ta hanyar fitar da mutane kusan miliyan 800 daga kangin talauci. A tsakanin shekarar 2013 zuwa 2021, alkaluman bankin duniya sun nuna cewa, ƙasar Sin ta ba da gudummawar da ya kai kashi 38.6 cikin ɗari ga tattalin arzikin duniya. Haka kuma a lokacin da duniya ke cikin annobar COVID-19 da kuma bayan cutar, ƙasar Sin ta kasance jigon ci gaba mai ƙarfi yayin da sauran manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ke fafutukar samar da ingantaccen ci gaban GDP.

Tattalin arzikin ƙasar Sin yana da matuƙar fa’ida. A yayin da tattalin arzikin duniya yake ƙaruwa da kashi 2.8 cikin ɗari a shekarar 2023. “Tattalin arzikin Sin ta kai kusan ninki biyu, a ƙalla fiye da kashi 4 cikin ɗari. Don haka, har yanzu tattalin arzikin ƙasar Sin na samun bunƙasuwa cikin sauri fiye da yawancin tattalin arzikin ƙasashen duniya.”

Ci gaba da zurfafa kasancewar kamfanonin ƙetare a kasuwannin kasar Sin, da zuba jari, shi ma ya kasance kyakkyawan aminci da cikakken kwarin gwiwar da ƙasashen duniya ke da shi game da bunƙasuwar tattalin arzikin ƙasar Sin.

Labarai Masu Nasaba

Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

Mummunar fahimtar da wasu kafafen yaɗa labarai na yammacin Turai ke yi ma tattalin arzikin ƙasar Sin ba zai yi tasiri ga yunƙurin dunƙulewar duniya waje guda da gano hanyoyin samun ci gaba da farfadowar tattalin arziki ba.

Ƙasar Sin ta kasance wata muhimmiyar madogara ga ci gaban tattalin arzikin duniya a cikin shekaru goma da suka gabata. Ƙasashen duniya dole su yi haɗin gwiwa tare da keta hazo don ciyar da tattalin arzikin duniya gaba.

Wannan dalili ne ya sanya yin adawa da ƙasar Sin tamkar ɓata lokaci ne. Kalmomi kamar “a guji” ko “a yi nesa” da ƙasar Sin sun zama sanannu a siyasar yammacin duniya, da aka yi amfani da su don ƙasashen yammacin duniya su ƙyamaci ƙasar Sin. Sai dai da’awarsu ba ta yi tasiri ba saboda ai “bindin raƙumi ya yi nesa da ƙasa”.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Amfanin Juna Shi Ne Tushen Hadin Gwiwar Afirka Da Sin

Next Post

Bangaren Sin Ya Taya Saliyo Murnar Gudanar Da Babban Zabe Cikin Kwanciyar Hankali Da Lumana 

Related

Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan
Daga Birnin Sin

Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan

13 hours ago
Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana
Daga Birnin Sin

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

14 hours ago
Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5
Daga Birnin Sin

Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

15 hours ago
Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu
Daga Birnin Sin

Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

15 hours ago
Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani
Daga Birnin Sin

Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

17 hours ago
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya
Daga Birnin Sin

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

1 day ago
Next Post
Bangaren Sin Ya Taya Saliyo Murnar Gudanar Da Babban Zabe Cikin Kwanciyar Hankali Da Lumana 

Bangaren Sin Ya Taya Saliyo Murnar Gudanar Da Babban Zabe Cikin Kwanciyar Hankali Da Lumana 

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya

July 28, 2025
Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar

Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar

July 27, 2025
Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan

Zhao Leji Ya Kai Ziyarar Sada Zumunta A Kyrgyzstan

July 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo

Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo

July 27, 2025
Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

July 27, 2025
Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

July 27, 2025
Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

July 27, 2025
Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

July 27, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Wasu Sojojin Bogi 2 A Legas

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yanbindiga Uku Da Kama AK-47 Guda Goma

July 27, 2025
Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

July 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.