Dakarun sojin kasar Bataliya ta 302 da rundunar sojin sama da jami’an tsaro na farin kaya na DSS da kuma ‘yan sanda sun tarwatsa sansanin kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafa (IPOB), a yankin Idara Nnebo, Ihe da na kauyukan Mbosi Ukpor da ke a Karamar Hukumar Nnewi ta Kudu da ke Jihar Anambra.
Daraktan yada labarai na na rundunar sojin kasa Birgediya-Janar Onyema Nwachukwuya ne, ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a yau Lahadi.
- An Gano Gawar Tsohon Jakadan Nijeriya A Amurka Da Ya Bace
- Zargin Cire Sashen Jikin Yaro: Jami’ar Lincoln Ta Dakatar Da Ekweremadu
Onyema, ya ci gaba da cewa dakarun sun kuma kwato malamai da suka hada da bindigar AK-47 guda biyu da kwabsar albarusai uku da albarusai masu karfin dango 7.62 da bindigu kirar gida da sauransu.
Ya kara da cewa sun tarwatsa sansanin ‘yan IPOB da ke cikin Dajin Nkwere a karamar hukumar Riba da ke a jihar Enugu, inda suka kwace mota kirar Toyota Highlander SUV daga gun wadanda ake zargin tare da kuma babbar bindiga da kwabsar albarusai bakwai.