Gwamnan Jihar Rivers da aka dakatar, Siminalayi Fubara, ya dawo jihar bayan hutun makonni biyu a ƙasashen waje.
Hakan ya zo ne yayin da kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Adaeze Oreh, ta ƙaryata zargin cewa ita ce ta jagoranci wasu matan jihar ficewa daga bikin Matar gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar, Mrs. Theresa Ibas, a wani taro a Fatakwal ranar Juma’a.
- Rikicin Ribas: Zarge-zargen Da Majalisa Ke Yi Wa Gwamna Fubara
- Ribas: Fubara Ya Fice Daga Gidan Gwamnati Yayin Da Sabon Shugaba Ke Shirin Karɓar Mulki
Fubara, wanda Shugaba Bola Tinubu ya dakatar a ranar 18 ga Maris, 2025, ya sauka ne a filin jirgin sama na Fatakwal da karfe 7:00 na yamma jiya Juma’a. Bidiyon da aka ɗauka na isowarsa ya nuna wasu daga cikin mashawartansa suna maraba da shi, kuma nan take aka tura wata mota ta ɗauke shi daga filin.
A wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, Dr. Oreh ta ƙalubalanci ƙungiyar ‘Concerned Rivers Youth Organisation’ da ta yi mata zargin da ta ce ta ba da tabbataccen hujja.
Ta ce: “Zargin da aka yi na cewa na shirya ficewar matan daga bikin Uwargidan Gwamna a ranar 2 ga Mayu 2025, karya ce kawai. Ba ni da hannu a cikin wannan lamirin kuma wannan ƙarya ce ta masu tada hankali.
“Na kasance na mai da hankali ne kan karatuna na digiri na uku a lokacin da aka dakatar da ni, ba tare da shiga cikin wani yunkuri ba. Ina kira ga duk masu ruwa da tsaki su taimaka wajen inganta zaman lafiya a jihar.”
Ta kara da cewa ta kasance tana aiki don ci gaban jihar kuma ta bukaci mutane su guji yada jita-jita maras tushe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp