Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Bayis Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya) a matsayin mai kula da Jihar Ribas, bayan ayyana dokar ta-baci a jihar.
Tinubu, ya ce; gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da ɗaukacin ‘yan majalisar dokoki na jihar za su dakata da gudanar da ayyakun gwamnati a jihar.
- Masu Zuba Jari Na Waje Suna Da Kyakkyawan Fata Game Da Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin
- Mutum 330 Sun Mutu Yayin Da Isra’ila Ta Kai Wa Gaza Sabbin Hare-hare
A bayanin kai tsaye da shugaba Tinubu, ya gabatar a gidan talabijin na ƙasa (NTA), ya ce; bangaren shari’a na jihar zai ci gaba da aiki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Tinubu ya bayyana fatansa cewa, wannan mataki zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da tsari a Jihar Ribas, tare da tunatar da duk masu ruwa da tsaki game da muhimmancin bin kundin tsarin mulki a Nijeriya.
Ribas, jiha ce da tasirin Siyasarta ya yi kamari, inda al’amura ke ta dagulewa a tsakanin Bangaren zartaswa a karkashin gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp