Hajiya Fatima Bature Dan’uwa, ita ce shugabar gidauniyar raba matasa da matsalar shaye-shayen miyagun Kwayoyi ta Kasa (YADAF).
Ta kasance ‘yar kishin Kasa mai rajin kawo sauyi ta fuskar nemo bakin zaren warware matsalar shaye- shaye da ke neman zamar wa Kasar nan Kadangaren bakin tulu. A tattaunawar ta wakilinmu, ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA.
Hajiya Fatima Bature ta bayyana matuKar damuwar ta bisa yadda matsalar shaye-shayen miyagun Kwayoyi suke neman zama ruwan dare a tsakanin matasa maza da mata. Ta kuma bayyana wasu abubuwan da sake haifar da wannan babbar matsala. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:
Za mu so ki gabatar wa mai karata kanki?
Alhamdulillahi, ni dai kamar yadda aka sani sunana Hajiya Fatima Bature Dan’uwa, an haife a Unguwar Gwale da ke cikin Birnin Kano. Na yi Karatun firamare da sakandire duk a Kano, sannan na yi digiri na farko da na Biyu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda na karanci ilimin aikin jaridar.
Mene ne dalilin kafa wannan Kungiya, musamman kasancewar ki mace?
Gaskiya lamarin shaye-shayen miyagun Kwayoyi ya zama wata matsala da kullum da ita nake kwana nake tashi, musamman kasancewar ina da Kani wanda ke da wannan matsala tun muna yara, duk da irin KoKarin da aka yi na kai shi gidajen lura da wannan matsala, sai da takai KwaKwalwarsa ta samu matsala. Wannan tasa tun da na taso matsala ta tsaya min a rai.
Dalilina na biyu kuma shi ne, yadda na hadu da wasu ‘yan mata guda biyu daga Adamawa da suka samu matsala da iyayensu, suka taho Kano bisa zaton samun taimako.
Wani ikon Allah sai suka fada hannun mugwayen samari da suka dora su a hanyar shaye-shaye, daga nan na nemo su na tafi da su Legas. Daya daman ta fara sakandire, na sama mata makaranta, gudan kuma ta koyi dinki, alhamdulillahi dukkansu Allah ya kubutar da su har sun yi aure.
Bisa irin tarbiyar da muka taso muka samu daga iyayenmu, ya sa na ga ni ma akwai gudunmawar da ya kamata na bayar domin magance wannan matsala. Kasancewa ta mace na tabbata matsalar shaye-shaye mu iyaye mata tafi damu, saboda mafi yawancin tarbiya a hannunmu take. Wannan ya sa bisa irin damar da Allah ya ba mu na ga ya dace in hada hannu da sauran mutane masu kishin kyautata rayuwar matasa wadanda sune manyan gobe.
Me kike ganin shi ne kanwa uwar gami wajen jefa matasa cikin al’amuran shaye -shayen miyagun Kwayoyi?
Gaskiya a irin binciken da muka gudanar, mun fahimci abubuwa masu yawa da ke haifar da matsalar shaye-shaye a tsakanin matasa. Da farko babu shakka rabuwar iyali na taka gagarumar rawa wajen jefa yara cikin wannan matsala, sai kuma abokai, wannan ko shakka babu shi ne ya zama kamar ruwan dare, zamantakewar unguwa, makarantu da sauran wuraren haduwa na haifar da irin wannan matsala idan aka yi rashin sa’ar samun nagartattun abokai.
Hakazalika, matsalar talauci na bayar da gudunmawa wajen tsintar kai cikin matsalar shaye-shaye, yawan tunani da rashin aikin yi duk suna cikin abubuwan da bincikenmu ya tabbatar mana da kasancewa cikin hanyoyin tsintar kai a wannan hali. Saboda Haka lallai akwai buKatar yi wa matsalar kallon tsanaki domin magance matsalar baki dayan ta.
Ganin yadda kuka yi wa matsalar filla-filla, shin ko ta ina wannan gidauniya ta fara nata aikin?
Alhamdulillahi, da farko mun fara daga matakin Karamar hukuma, inda muka fara da Ungogo da Nasarawa.
Kamar yadda kuka sani duk wata Kungiya ko gidauniya da aka kafa ta, kuma ake fatan dorewarta, dole a samar mata da manufofin da tsare-tsare wanda za a tafiyar da ita akansu.
Wannan gidauniya mai zaman kanta ce, saboda haka akwai abubuwa da muka tsara kuma muke tafiya akansu. Da farko dole irin wannan gidauniya ta samu kyakkawar alaKa da hukumomin tsaro da na gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, wannan tasa muka fara ziyarar zumunci ga hukumomi, musamman irin su NDLEA, masarautu da sauran hukumomi domin gabatar da manofofin gidauniya tare da bayyana masu ayyukan da muka sa a gaba.
Kasancewar ayyukan wannan gidauniya ya shafi bangarori daban-daban, shin ko ina ne matsuguni wannan gidauniya?
Gaskiya ne, kamar yadda na fada tun da farko, wannan gidauniya na da ofis a Safiya House daura da Masallachin Juma’a na Umar Ibn Khattab da ke kan titin Zariya a Jihar Kano, sannan mun kasa ofishin kashi biyu, akwai bangaren gudanar da harkokin mulki da kuma sashin horarwa, fadakarwa da koya sana’o’in dogaro da kai.
Yanzu haka mun kawo kwamfutoci da kekunan dinki wanda za mu fara da su da yardar Allah.
Wani abin sha’awa za a dinga koyarwa lokaci biyu a rana, sannan daliban nan za su dinga cin abinci.
Kasancewa masu wannan matsala na da wahalar sha’ani, shin ko ta yaya kike iya samun haduwa da su domin fahimtar matsalolinsu?
Alhamdulillahi, muna da ma’aikatan da ke zagawa cikin al’umma tare da ziyartar wuraren da masu wannan matsala ke tsugunnawa, inda ake amfani da hikimomi ta yadda za a ja hankalinsu.
A lokuta da dama sukan biyo mu har ofis mu tattauna da su tare da ba su shawarwari, wani lokacin kuma mukan samu gayyata daga iyaye, inda muke zuwa har gida mu zauna da su da kuma su iyayen nasu mu tattauna, sannan wani lokacin mu kan ziyarci makarantu, inda muke fadakar da su illolin ta’ammali da miyagun Kwayoyi, sai mu dan raba masu kyaututtukan kayan karatu da makamantansu.
Yaya dangantaka take tsakanin wannan gidauniya da masarautu da malamai magada annabawa?
Kamar yadda na fara ambatawa, yana daga cikin manufofin wannan gidauniya mu kan gudanar da ziyarce-ziyarce domin sanar da su ayyukanmu, kuma alhamdulillahi suna ba mu hadin kai kwarai da gaske.
Mene saKonki ga jama’a musamman iyaye?
Babban sakona bai wuce cewa jama’a su daina kyamar masu dabi’ar shaye-shayen muyagun Kwayoyi, sannan a Kara taimaka mana da addu’o’I, kuma iyaye su Kara himma wajen kula da tarbiyar ‘ya’yansu, musamman abonkan mu’amalar yaran nasu. Muna Kara kira ga matasa su fahimci illar ta’ammali da miyagun Kwayoyi.