Fitaccen malamin addinin musulunci da ke jihar Kano, Dakta Abdallah Gadon-Ƙaya ya yi amai ya lashe kan zargin da ya yi na cewa, wasu gungun masu auren jinsi da luwaɗi da maɗigo sun taru a jihar Bauchi domin sheƙe ayarsu a kwanakin baya.
Malamin ya fito ɓalo-ɓalo ya janye kalamansa tare da bai wa al’umma musamman musulmai haƙuri bisa furucin nasa.
- Kwangilar Biliyan 30: PDP Ta Bukaci EFCC Ta Binciki Gwamnatin Sakkwato
- Ambaliyar Ruwa Ta Katse Hanyar Maiduguri Zuwa Damboa
Gadon-Kaya ya ce, bisa zurfafa bincike da gwamnatin jihar Bauchi da hukumomin tsaro suka yi, an tabbatar da cewa labarin da ya bayar ƙarya ce sam babu wani auren jinsi da aka taru daga jihohi domin yinsa a jihar Bauchi.
Idan za a tuna dai malamin ya taɓa shelanta wa duniya cewa, wani mutumi ya kirasa ya tabbatar masa da cewa, ana auren jinsi da luwaɗi da maɗigo a wani otel da ke jihar Bauchi. Malamin har ya ce yana da hujja da sunan otel ɗin kuma zai iya bayarwa idan aka nema.
Sai dai bayan da gwamnatin jihar Bauchi ta hannun hukumar Shari’a da ta nemi malamin domin ya zo ya gabatar mata da hujjojin nasa da kuma inda abun ya faru sai ya janye kalaman nasa.
Kan hakan ne malamin ya fito cikin wani faifayin bidiyo mai tsawon mintuna fiye da biyar ya na bai wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad da jami’an gwamnatin da hukumomin tsaro haƙuri bisa bayanin da ya fitar da ya tada hankalin jama’a da daman gaske.
Ya ce: “A satukan da suka gabata, akwai bayanin da na yi a kan labari da wani bawan Allah ya ba ni a kan faruwar wani taron auren jinsi a jihar Bauchi. Na ce ya kirani ya bani bayani cewa ga abun da ke faruwa cewa a yi wa’azi a faɗakar kuma a yi bincike.
“To, mun yi wannan maganar kuma maganar ta yaɗu kuma muka ce a bincika hukuma ta ɗauki mataki. Hukuma ta bincika, jami’an tsaro sun bincika babu wannan auren jinsin kuma ba a yi shi ba a jihar Bauchi.”
Ya ce suna godiya wa Allah bisan rashin faruwar hakan, domin a cewarsa, hakan ma alkairi ne domin ba a samu faruwar ɓarnar ba.
Ya jinjina wa irin ƙoƙarin da jami’an tsaro da gwamnatin jihar Bauchi suka yi wajen bincikawa sosai har suka tabbatar da babu faruwar wannan labarin kwata-kwata.
Ya nuna cewa, a sakamakon kalaman nasa, rayukan dubban mutane sun ɓaci musamman wadanda suke kishin musulunci a ko’ina suke.
“Don haka, muna amfani da wannan damar tun da bincike ya tabbatar da ba a yi wannan abun ba, muna bada haƙuri ga duk wanda wannan abun ya shafe shi tun daga kan mai girma gwamna a matsayinsa na uba kuma jagora a wannan jihar da sauran muƙarrabansa da na kusa da shi, da jami’an tsaro da dukkan sauran al’umma baki daya.
“Mu yi haƙuri dukkanmu. Saboda ita da’awar haka ta gada wani lokacin za a iya faɗan wani abun wani lokacin ya zama haka ne wani lokacin ya zama ba haka ba ne, to daman ba fata muke abun ya faru ba. Allah ya bai wa kowa haƙuri baki ɗayanmu, Allah ya sa muma mu dace.
“Allah shi ne shaida ba mun yi wannan abun saboda cin zarafi ko ɓata wani ko kuma cin mutuncin wani, kwata-kwata babu wannan a tare da mu. Wallahi kishin jihar ce. Ni ɗan Bauchi ne, halastaccen ɗan Bauchi. Zan iya bayar da duk abun da na mallaka da rayuwata don na kare wannan jihar tawa na taimaki addini na taimaki da’awa.”