Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta ce ta kammala shirye-shiryen yaye dalibai 11,000 karo na 38 a tarihin Jami’ar.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Abbas ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Kano.
Abbas ya ce, a yayin bikin, dalibai 180 sun kammala karatun digiri da daraja ta daya, 3,770 sun kammala karatun digiri na biyu (Masters), sai kuma dalibai 370 da suka kammala digiri na uku.