Dalibai 2,199 daga suka fito daga kananan hukumomin Musawa da Matazu suka amfana da tallafin karatun dan majalisar wakiltar kananan hukumomin Musawa Hon. Abdullahi Aliyu.
Tallafin na da nufin ragewa dalibai kudin rijista a daidai lokacin da ake fama da matsalolin rayuwa na yau da kullum musamman a yankunan karkara.
- Gwamnan Bauchi Ya Gabatar Da Naira Biliyan 878 A Matsayin Kasafin 2026
- Sin Ta Kasance Mai Goyon Bayan Kasashen Afirka Wajen Zamanantar Da Kansu
Haka kuma daliban sun hada da masu karatu a kwalejin kimiyya da fasaha ta Katsina Poly da kwalejin gwamnatin tarayya ta F.C.E Katsina da Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da kwalejin kimiyya ta ICT Katsina
Bada tallafin ya gudana a karkashin kwamitin ilmin dan majalisar wanda tsohon mataimakin gwamna Alhaji Tukur Ahmad Jikamshi ke jagoranta.
Da yake jawabi a wajen taron raba tallafin dan majalisar wakilai na kananan hukumomin Musawa da Matazu Hon. Abdullahi Aliyu Dujiman Katsina ya bayyana dalibai 1,029 sun fito ne daga jami’o’i wanda kowane zai samu tallafin Naira ₦30, 000 wanda kudin suka kama miliyan 30,870,000
Ya kuma kara da cewa kimanin dalibai 1,170 sun fito ne da kwalejin gwamnatin tarayya da kuma na jihohi inda kowa zai samu tallafin Naira ₦20,000 inda za a ba su Naira miliyan 23,400 baki dayan su.
Hon. Abdullahi Aliyu Dujiman Katsina ya ce an kashe kimanin naira miliyan 54,270,000 a matsayin tallafin kudin rijista a makarantun gaba da sikandire ga mutane 2,199 da suka fito daga kananan hukumomin Musawa da Matazu
“Yanzu mun maida hankalinmu akan shirye-shirye da tsare-tsaren samar da makoma mai kyau ga matasa acikin al’umma musamman abinda ya shafi harkar ilmi da kiwon lafiya da sauran su ‘ inji shi
Shugaban kwamitin ma’aikatar cikin gida, ya kara da cewa zai cigaba da riɓanya kokarin sa na ganin an inganta rayuwar matasa ta hanyar sama musu aikin yi da tallafi domin yin sana’a domin dogaro da kan su.
Haka kuma ya yi alkawarin samarwa matasa 420 da suka fito daga kananan hukumomin Musawa da Matazu aikin yi domin rage zaman kwashe wando a tsakanin matasa.
Idan za a iya tunawa dan majalisar ta samarwa matasa aikin yi a hukumar kashe gobara ta kasa da Asibitin koyarwa ta Katsina da ‘yan sanda da sojoji da hukumar shige da fice ta kasa (immigration) da hukumar tsaro ta sibil difans.
A cewar sa, nan bada jimawa ba, zai raba mashina guda 500 ga matasa da suka fito daga kananan hukumomin Musawa da Matazu domin a samu saukin zirga-zirga a wannan yankuna.
” Babban abinda ke gabana yanzu shi ne matasa inasan in ga rayuwar matasa ta canza daga halin da suka tsinci kansu a wannan lokaci da ake fuskantar matsalolin rayuwa na yau da kullum” inji shi
Tunda farko da yake jawabi shugaban karamar hukumar Musawa Hon. Aliyu Idris Gingin ya bayyana tallafin a matsayin wani kaɓakin arziki da zai taimakawa harkar ilmi karkashin inuwar dimokuradiyyar
Ya kuma kara da cewa hakan zai taimaka wa daliban wajen bunkasa ilimin su sannan Dujiman Katsina ya kama hanyar da gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda ya dora gwamnatin sa akan ke nan.














