• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daliban Kano Da Bauchi Sun Lashe Gasar Alkur’ani Ta 2023

by Sadiq
2 years ago
Alkur'ani

Zainab Aliyu Muhammad daga Jihar Kano ta zama gwarzuwar gasar Alkur’ani ta kasa ta shekarar 2023 a bangaren mata a hadda da tafsiri.

A bangaren maza kuwa, Ibrahim Muhammad Nasir daga Jihar Bauchi ne, ya zama gwarzon shekara a musabakar karo na 38, wadda aka kammala a Jihar Yobe.

  • Hare-Hare: Gwamnatin Filato Ta Ayyana Zaman Makokin Mako Guda
  • Ba Za Mu Lamunci Lalaci Daga Waɗanda Aka Naɗa Muƙamai Ba– Tinubu

Mai masaukin baki, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karamma Zainab Aliyu Muhammad daga Jihar Kano da kyautar mota kirar Honda Accord.

Ibrahim Muhammad Nasir kuma gwamnan ya gwangwaje shi da kyautar mota kirar Honda Accord.

Sannan ya ba da kyautar bas mai daukar mutane 18 kirar Toyota Hummer ga kwamitin shiryar musabakar na kasa don ci gaba da dawainiyar gasar Alku’rani.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

A ranar Asabar ne aka kammala gasar karatun Alkur’anin ta kasa karo na 38 a Damaturu, Jihar Yobe inda alarammomi daga sassan Nijeriya suka nuna bajintarsu.

A lokacin rufe gasar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yaba wa matasan da suka shiga wannan gasar ta karatun Alkur’ani Mai Girma rukuni-rukuni, sannan ya yi musu fatan alheri.

Sarkin Musulmi, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya nuna farin cikinsa bisa yadda aka gudanar da gasar a Yobe cikin kwanciyar hankali kuma a bisa tsari ba tare da an samu cikas ba.

Shi ma shugaban Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Lawan Sulaiman Bilbis, ya yaba wa gwamna Mai Mala Buni bisa yadda ya dauki nauyin gasar da kuma yadda aka gudanar da ita cikin nasara.

Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Danfodiyo ce, ke shirya gasar tasa a Nijeriya, kuma wannan shi ne karo na 38.

Mahalarta bikin rufe gasar ta Alkur’ani sun hada da Gwamna Jihar Gombe, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, Mataimakin Gwamna Jihar Borno, Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba.

Sai masu girma sarakunan Jihar Yobe gaba daya, karkashin Mai Martaba Sarkin Fika, sai Mai Martaba Shehun Dikwa da ya wakilci Mai girma Shehun Borno, sai Mai girma Sarkin Bauchi da sauran manya-manyan baki.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati
Labarai

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba
Labarai

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Next Post
Tinubu Ya Dakatar Da Halima Shehu, Ya Nada Akindele Egbuwalo A Matsayin Kodinetan NSIPA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.