Kungiyar malaman jami’o’in Nijeriya (ASUU), ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21, inda suka yi gargadin tsunduma yajin aiki na gama gari.
Shugaban kungiyar ASUU reshen jami’ar Gashua da ke a Jihar Yobe, Melemi Abatcha ya bayyana haka a taron manema labarai da kungiyar ta kira a garin Damaturu, babban birnin jihar.
- Yadda Ambaliya Ta Lalata Gidaje 255 A Garin Natsinta Da Ke Katsina
- PCACC Ta Kama Shugabannin Ƙananan Hukumomi 3 Bisa Zargin Almundahanar Miliyan 660
Kazalika, Melemi ya zayyana wasu manyan batutuwan da suke ci gaba da janyo wa fannin ilimin koma baya da suka hada da rashin wadatattun kudade na tafiyar da jami’o’in kasar da kuma gaza cika yarjejeniyar 2009.
A nan ga manyan daililai biyar da suka sanya kungiyar ta yi barazanar sake shiga yajin aikin na gama gari wadanda suka hada da; rashin samar wa da jami’o’in kasar wadatattun kudade, rashin samar masu da kayan aiki.
Sauran dalilan su ne; rashin isassun malamai, wuraren kwanan dalibai, rashin samar da kayan yin gwaje-gwaje da kuma dakunan karatu.
Kungiyar ta nuna bacin ranta a kan rashin cika alkawarin yarjejeniyar 2009 da kuma jinkirin da ake samu daga bangaren gwamnati kan yarjejeniyar, wanda hakan ya janyo ake ci gaba da biyan malaman jami’ar albashi mafi inganci.
A kan dambarwar tsarin biyan albashin maIaman jami’o’in na IPPIS duk da umarnin da majalisar zartarwa ta bayar a shekarar 2023, na a cire kungiyar daga cikin tsarin, har zuwa yanzu ana biyan ‘ya’yan ASSU ta hanyar wannan tsarin, wanda kungiyar ta bayyana cewa ba za ta lamunci hakan ba.
Haka kuma kungiyar ta nuna rashin jin dadinta kan rashin bai wa jami’o’in damar cin gashin kansu da kuma ci gaba da kirkiro da jami’o’in da gwamnati ke yi wanda hakan ke sanyawa ba a samun ingantaccen ilimi a kasar nan.