Idan aka yi la’akari da canjin da aka samu a cikin karamin lokaci, akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa za a iya jinkirta zaben shugabannin majalisar ta 10 wanda za a kaddamar a ranar Talata, 13 ga Yunin 2023.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa LEADERSHIP cewa, ganin yadda takun saka a tsakanin zababbun ‘yan majalisar da ke goyon bayan ’yan takarar jam’iyyar APC mai mulki a zauren majalisar ta 10 da kuma masu bijire masu. Sabanin umarnin jam’iyya mai mulki, ana iya dakatar da zaben shugabannin majalisun guda biyu, wanda hakan na iya kawo jinkiri wajen kaddamar da majalisa ta 10, kamar yadda magatakardar majalisar dokoki ta kasa (CNA), Sani Magaji Tambuwal ya shelanta kan kaddamar da sabuwar majalisar, wanda za a iya jinkinta na wani dan lokaci.
Wasikar shelan daga shugaban kasar wata makami ce da za ta bai wa magatakardar damar damar ci gaba da jan ragamar jagorancin majalisa ta 10 kafin zaben shugabanni.
Majiyar daga wurin manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, sun shaida wa wakilinmu cewa, dabarar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai yi amfani da shi idan aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa shi ne, zai yi amfani da damarsa wajen hada kan ‘yan majalisar jam’iyyar APC wadanda ake ganin masu tayar da kayar baya a zauren majalisan domin kaucewa samun baraka kamar yadda jam’iyyar ta samu a 2011 da 2015.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa an bayyana zababben sanata daga yankin kudu maso kudu, Sanata Godswill Akpabio da kuma Sanata Barau Jibril daga Arewa maso yamma a matsayin ‘yan takarar da jam’iyyar APC ta tsayar a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa. Yayin da aka zabi Tajudeen Abbas daga Arewa maso yamma da Benjamin Kalu daga kudu a matsayin shugabanm majalisar wakilai da mataimakinsa.
Rashin gamsuwa da hukuncin jam’iyyar na rashin tuntubar masu ruwa da tsaki tasa, Sanata Abdul’aziz Yari daga Arewa maso yamma da shugaban mai tsawatarwa na majalisar dattawa mai ci, Sanata Orji Uzor Kalu daga kudu maso gabas da zababben Sanata Osita Izunaso daga kudu maso gabas sun sha alwashin tsayawa takarar shugaban majalisar dattawa, domin kare ’yancin majalisar kamar yadda kundin tsarin mulki na 1999 da kuma dokar majalisar dattawa suna tanadar.
Har ila yau, Sanata Sani Musa daga shiyar Arewa ta tsakiya ya kalubalancin tsarin karba-karba na jam’iyyar APC, wasu zababbun ‘yan majalisu daga yankin Arewa ta tsakiya sun mara masa baya domin neman kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa a kan zaben da jam’iyyar ta tsayar da Barau.
A halin da ake ciki kuma, akwai rahotannin da ke cewa Yari da Kalu da Izunaso su uku na tunanin kulla kawance da tsohon gwamnan Jihar Zamfara a matsayin dan takarar da zai fafata da Akpabio tare da goyon bayan wasu tsirarun zababbun ‘yan majalisar ta 10 da ba a kaddamar da su ba.
Hakazalika, a zauren majalisar wakilai da ba a kaddamar ba, mambobin G6 da suka hada da mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Idris Wase daga yankin Arewa ta tsakiya da Hon. Mukhtar Aliyu Betara daga Arewa ta gabas da Hon. Miriam Onuoha daga kudu ta gabas da Hon. Yusuf Adamu Gagdi daga Arewa ta tsakiya da Hon. Aminu Jaji daga Arewa maso yamma da kuma zababben dan majalisar Sada Soli Jibia daga Arewa maso yamma sun sha alwashin samar da dan takara daya tilo daga cikinsu domin ka da APC ta zabi Abbas.
Hukuncin da Yari, Kalu da Izunaso a gefe guda da kuma G6 a majalisar wakilai suka yi na ci gaba da tayar da kura bayan da shugabannin jam’iyyar APC na kasa suka yi watsi da alkawarin da suka yi musu na duba tsarin karba-karba mai cike da ce-ce-ku-ce da jam’iyyar ta dauka.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa tuni harsashi ke ta yawo kan zaben Sanata Barau a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa da kuma Hon. Abbas a matsayin shugaban majalisar wakilai a daidai lokacin da su biyun suka fito daga shiyyar Arewa maso yamma, yayin da jam’iyyar APC ta yi watsi da yankin Arewa ta tsakiya a tsarin karba-karbanta.
Zababben sanatan Zamfara ta yamma, kuma dan takarar shugabancin majalisar dattawa, Abdul’aziz Abubakar Yari ya nuna rashin amincewarsa da tsarin shiyya-shiyya na jam’iyyar APC mai mulki a majalisar dattawa ta 10 a kan cewa ya ci karo da kundin tsarin mulkin na 1999 wanda aka yi wa gyaran fuska.