Wannan rubutu na yi shi ne saboda korafe-korafen jama’a masu ta’ammuli da na’urorin Kwamfuta da manyan wayoyin hannu da kullum ake amfani da su domin gudanar da al’amuran yau da kullum.
Ta’ammuli da Kwamfuta ko wayar hannu ya zamo jigo a rayuwar jama’a domin gudanar da aiyukan yau da kullum, kama daga kasuwanci, fannin ilimi, fannin lafiya, bincike-bincike, fannin tsaro, ayyukan kotu, fannin yada labarai da sauran al’amura masu yawan gaske.
- Zama Lafiya Ya Fi Zama Dan Sarki
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Matsayinta Na Warware Matsalar Ukraine A Siyasance
Ilimin sarrafa kwamfuta da wayar hannu ya zama mai saukin gaske. Ganin yadda ake ta kara inganta su da kuma saukaka fahimtar yadda za’a sarrafa su ko da mutum ba shi da ilimin zamani a halin yanzu, za a ga kusan kowa yana da wayar hannu ko kwamfuta koma dukkansu biyu, babu babba babu yaro.
Yawaitar amfani da na’urori domin bukatun yau da kullum, yana da alaka da saukin mallakarsu, ko da yake masu iya magana sunce, iya kudinka iya shagalinka. Dukkanin wadannan na’urori sun yi tarayya wajen abubuwa kamar haka; saurin sarrafa aiki, rumbun adana abubuwa ko kayan da aka sarrafa, ababen dogaro lokacin gudanar da aiki, saukin dauka ko rikewa a hannu lokacin zirga-zirga da sauran al’amura.
Idan ba a samu abubuwa biyu zuwa uku daga cikin wadancan siffofi da na bayyana ba, yakan haifar da damuwa wajen sarrafa na’ura. Kwamfuta da wayar hannu sukanyi nauyi ko jinkiri wajen sarrafa aiyuka, saboda dalilai masu yawa. Amma zan yi bayani a kan wadanda suka fi muhimmanci.
Akwai cutar na’ura mai yaduwa (Birus), sanin kowane cutar na’ura ta bairos da ire-irensu suna taka rawa wajen sauya akalar sarrafa na’ura, sukan cutar da ita, suna hana ta yin aiki kamar yadda aka tsara ta, sai taki gaba taki baya. Amfani da manhajar maganceta (anti-birus) yana da matukar muhimmanci.
Wasu sukan cunkushe na’ura da manhajoji ba bisa ka’ida ba. Akwai wadanda suke akidar saka manhajoji iri-iri masu yawa ko da basu iya aiki da su ba. Yin hakan yana haddasa cunkushewar rumbun adana aiki (memory). Saboda cire manhajar da ba’a amfani da ita yana bunkasa aikin na’ura cikin sauri.
Yin amfani da na’ura a cikin yanayi mai zafi ko waje maras isashshiyar iska yana haddasawa sassan ita na’urar jinkirin aiki. Wanda hakan yana jawo koma baya ga ingancin na’ura. Dan haka idan babu na’urar sanyaya daki sai a kunna fanka, idan ita ma babu to sai a bude kofofi da wunduna domin iska ta dinga ratsa su a lokacin da ake aiki.
Idan ba a sabunta manhajoji a kan lokaci, to wannan ma babban al’amari ne da yake jawo tarnaki ga na’ura. Sabunta manhaja (update) a kan lokaci yana da amfani domin yana magance duk wata matsala tattare da ita kanta manhajar da sauran sassan na’ura dake aiki da manhaja lokacin gudanar da aiki.
Yin amfani da gurbatattun manhajoji (applications) na da illa ga na’ura. Domin yakan yi sanadiyyar bude dukkan kofofin sirri na na’ura domin cututtuka masu yawa su shiga. Kuma sukan zamo makamai da masu kutse ke amfani dasu wajen cutar da al’umma. Kuma an fi samun su a manhajoji na kyauta (free). Amfani da sahihan manhajoji shi ne mafi da cewa ga jama’a.
Barin datti ko kura a cikin na’ura, wato rashin tsaftace na’ura ko dakunan da ake amfani da ita, harma da teburin da aka dorata idan ta girke ce (desktop), yana da matukar illa wajen toshe kofofin shakar iska ga ita na’urar, har ma lalacewar wasu sassa saboda tsabar datti da kura. Saboda haka kula da tsaftar na’ura yana inganta sassanta yadda za ta yi aiki cikin sauki.
Fuskantar katsewar wutar lantarki a lokacin da ake tsakiyar aiki da na’uara, ko kwamfuta ta mutu saboda batir babu isashshen caji, babbar matsalace. Hakan yana haddasa matsala ga rumbun adana aiki (Hard Disk Dribe) kuma yana haddasa jinkiri wajen gudanar da aiyuka. Amfani da na’urar adana wutar lantar ki (UPS) da kuma isashshen caji ga wayoyi ko kwamfuta Laptop, zai taimaka kwarai. Ana so idan an dauke wuta sai a kashe a hakura har sai an sami wuta ko kuma a tayar da Janareto.