Ministan Ma’aikatar Bunkasa Kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ya sanar da cewa; gwamnatin tarayya ta shirya tsaf, domin mayar da wuraren kiwo 417 zuwa wajen kiwo na zamani.
Ya ce, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne, domin bunkasa fannin kiwo da kuma rage yawon da Shanu ke yi kan titunan kasar nan da sunan kiwo.
- Dalilin Da Ya Sa Tinubu Ya Nada Jega A Matsayin Mai Ba Shi Shawara Kan Samar Da Sauyin Noma Da Kiwo
- Kasar Sin Ta Nanata Adawa Da Matakan Tilastawa Da Nuna Babakeren Tattalin Arziki
Ya bayyana hakan ne, a lokacin da tawaga daga Cibiyar Binciken Aikin Gona ta kasa (ARCN), ta kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja, ranar Alhamis da ta gabata.
Babban Sakataren Cibiyar, Garba Sharubutu ne ya jagoranci tawagar a lokacin ziyarar.
Maiha ya kuma umarci Cibiyar, ta kara kaimi wajen gudanar da bincike da kuma yin aiki da fasahar kere-kere, domin kara habaka fannin na kiwo.
A wani labarin makamancin wannan, kimanin kananan masu kiwo 100 ne a Jihar Kwara, suka amfana da tallafin kiwon Awaki na kashin farko.
Wannan tallafi, na daga cikin dabarun gwamnatin jihar na son kara bunkasa fannin da kuma samar da kudaden shiga ga masu kiwon, domin samun riba.
A jawabinta a garin Ilorin, wajen kaddamar da kashin rabon Awakin, kashi na farko; wato a karkashin shirin jin kan iyali na L-PRES, Kwamishin Bunkasa Kiwo, Oloruntoyosi Thomas ya sanar da cewa, masu ruwa da tsaki a fannin ne, suka bayar da tallafin Awakin
Thomas ya sanar da cewa, kwalliya na biyan kudin sabulu dangane da shirin L-PRES a jihar ta Kwara.
Ta sanar da cewa, Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak, ba wai kawai yana yin wadannan abubuwa ba ne don bayar da horo a bangaren kiwo a jihar, har da ma bukatar da yake da ita ta son ganin ‘yan jihar, suna samun kudaden shiga, musamman domin inganta tattalin arzikinsu da kuma na jihar baki-daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp