Wasu daga cikin masu kiwon Kajin gidan gona a Jihar Kano, sun fito da wata sabuwar dabara ta hada kai da wasu kananan masu kiwon Kajin gidan gona a jihar.
Masu kiwon, musamman wadanda ke kyankyashe ‘ya’yan Kajin kai tsaye da kuma wadanda ba kai tsaye suke kyankyashewa ba, na sayar da ‘yan tsakin da aka kyankayshe musu kwana daya da kyankyasa, wanda daga baya kuma bayan mako biyu ko uku, sai su koma wurin masu kananan kiwon da suka sayarwa, su sake sayen ‘yan tsakin, kafin su kammala girma.
- EFCC Za Ta Binciki Yadda Kudaden Kananan Hukumomi Ke Sulalewa
- Shugabannin Sin Da UAE Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 40 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya Tsakaninsu
Guda daga cikin masu kiwon Kajin a jihar, Malam Shehu Caji; ya sanar da cewa, rungumar wannnan sabuwar dabara ta zama dole, musamman don ganin sana’ar tasu ta ci gaba da dorewa.
A cewarsa, mun rungumi wannan sabuwar dabara ce; domin duba yadda ake ci gaba da samun hauhawar farashin abincin Kaji a fadin wannan kasa.
Shehu ya kara da cewa, a yanzu buhun abincinsu da ake fara ciyar da su mai nauyin kilo 25; ya kai Naira 20,700, sabanin Naira 10,000 da ake sayar da shi a shekarar da wuce.
Ya ci gaba da cewa, rungumar wannan dabara; ko shakka babu ta zama dole, domin a hankali fannin yana kara mutuwa ne, inda ya sanar da cewa, akasarin kwararrun da suke a cikin sana’ar na da yakin cewa, tuni fannin ya riga ya mutu, wanda hakan ya sanya suka dakatar da sana’ar baki-daya.
A cewarsa, mai kiwon zai sayi ‘yan tsakin da aka kyankyashe a kwana daya, sai ya ci gaba da kiwata su har zuwa daga mako biyu zuwa uku, sai kuma ya sake mayar da su inda aka sayo su, sai su kuma su sake saye daga wurinka, ma’ana; kamar kana jujjuya saye da sayar da su ne.
Ya sanar da cewa, wannna dabara ita ce yanzu ake amfani da ita wannan fanni na kiwon Kajin gidan gona; wadda kuma ta na ci gaba da tafiyar da fannin, amma ga wanda ya rungume ta.
Kazalika, rahotannin sun bayyana cewa; akasarin manoma yanzu, sun rungumi wannan babbar dabara.