A wani yunkuri na dakile katsalandan siyasa a bangaren shari’a, shugabar kotun daukaka kara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta mayar da dukkan kararrakin zaben da ke gaban kotun na jihohi 36 guda 1,209 zuwa rassanta na Abuja da Legas.
Don haka, an shaida wa LEADERSHIP cewa duk wasu kararrakin da suka taso daga hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe a jihohi 36 na kasar nan za a saurare tare da zantar da hukunci a rassan kotun daukaka kara da ke Abuja da Legas.
- Zaben 2023: Takaddamar Kashi 94 Cikin 100 Na Kujerun Da Aka Lashe Ta Dora Shakku Kan INEC
- Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Kudurin Dokar Bude Iyakokin Nijeriya Da Nijar
Bisa daukar wannan mataki da Dongban-Mensem ta yi, rassan kotun daukaka kara guda biyu ne kawai daga cikin 20 za su tantance duk wasu kararrakin da suka taso daga hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe a fadin kasar nan.
Umurnin ya shafi zabukan gwamnoni, na ‘yan majalisar tarayya da na jihohi, wanda aka shigar a gaban kotun daukaka kara bayan da kotun sauraron kararrakin zabe ta zantar da hukuncinta.
Wata majiya mai tushe daga shalkwatan kotun daukaka kara da ke Abuja ta bayyana cewa, dukkan kararrakin da suka taso daga hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe guda 1,209 da aka shigar kan zaben 2023, an tura su Abuja da Legas domin saurare da zantar da hukunci.
Tuni dai aka bukaci dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu, wadanda suka daukaka kara da su bayar da hadin kai kan wannan umarni ta hanyar komawa ko dai Legas ko Abuja domin ci gaba da shari’arsu.
Binciken da wannan jarida ta yi ya nuna cewa Dongban-Mensem ta yi hakan ne a matsayin martani ga dimbin koke-koke da zanga-zangar da jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu suka yi, inda suke zargin alkalan kotun sauraron kararrakin zabe da hada kai da gwamnonin wajen karkatar da gaskiya a lokacin shari’a a jihohinsu.
Jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyun adawa biyu, PDP da LP da fusatatun ‘yan takararsu sun koka a cikin korafe-korafe daban-daban ga shugabannin kotun daukaka kara kan yadda alkalan kotunan sauraron kararrakin zabe suka hada kai da gwamnoninwajen takwara shari’ar zabe domin goyan bayansu.
Wannan yana daga cikin babban dalilin da ya sa Dongban-Mensem ta dauki mataki domin tsaftace bangaren shari’a.
Rahotanni sun bayyana cewa za a gurfanar da wasu alkalan kotunan sauraron kararrakin zabe a gaban hukumar kula da harkokin shari’a ta kasa (NJC) domin su fuskanci hukunci.
LEADERSHIP ta gano cewa, Dongban-Mensem ta dauki matakin mayar da duk wasu kararrakin zabe da aka shigar a kotun daukaka kara zuwa Abuja da Legas sakamakon korafe-korafen aka shigar.
Don haka, sashen kotun daukaka kara na Abuja ne zai saurara tare da zantar da hukunci kan duk wasu kararrakin zabe da aka shigar a jihohi 19 na yamkin arewacin Nijeriya.
Haka zalika, hukuncin da suka fitowa daga kotun sauraron karar zabe na jihohi 17 da ke kudancin Nijeriya, bangaren kotun na Legas ne zai saurara tare da zantar da hukunci.
Ban da haka, an gano cewa Dongban-Mensem ta tabbatar da cewa matakin zai tabbatar da ‘yancin kan bangaren shari’a, musamman kotun daukaka kara.