Kungiyar dillalan mai ta kasa (lPMAN) ta bayyana dalilin da ya sa aka samun karancin man fetur ta yadda ‘yan kasuwan suke shan wahala wajen samun canjin kudade na kasashen waje.
Babban jami’in gudanarwa na kungiyar lPMAN, Mike Osatuyi shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Legas ranar Lahadi da ta gabata.
- CMG Ya Lashe Lambobin Yabo 4 Na Watsa Shirye-shirye Na Gasar Wasannin Olympics Ta Beijing 2022
- Gwamna Zulum Ya Bayar Da Umurnin Cafke ‘Ƴan Bangar Siyasar Borno
Mista Osatuyi ya kara da cewa ya zama wajibi su bayyana wa mutane yadda aka samu karancin man fetur sakamakon dogon layi da kuma wahala wajen samun mai a wasu sassan Nijeriya.
Ya zargi kamfanin mai na kasa (NNPC) da dakatar da shigo da isassan mai da zai wadata kasar nan. Mista Osatuyi ya jaddada cewa a halin yanzu ‘yan kasuwa ba za su iya ci gaba da sayar da man kan farashin da aka kayyade ba, saboda rashin daidaituwar farasha a ma’aciyar man.
“Muna fuskantar karancin mai sakamakon babu man da yawa. A halin yanzu farashin man a ma’aciyar man na masu zaman kansu yana tsakanin naira 205 zuwa naira 210, sabanin a baya da ake sayar da shi kan naira 162.50.
“Kamfanin NNPC shi ne kadai yake dauko tataccen man daga waje, wanda hakan ke yi wa ‘yan kasuwan wahala samu,” in ji shi.
Mista Osatuyi ya ci gaba da cewa ‘ya’yan kungiyarsu suna sayan mai duk lita daya a kan naira 200 a ma’aciyar mai ta masu zaman kansu, wanda hakan zai yi musu mahala su yawar da man kan kayadaddan farashi.
“Bayan haka, wannan yanayin ya bai wa masu ma’aciyar mai damar sayar da man fiye da farashin gwamnati.
“Lokacin da muka hada da kudaden sufuri da kuma riba, sai kowacce lita daya ta kasance a kan naira 217. Saboda haka nawa ake so ‘yan kasuwa su sayar da man, sannan kuma muna yin wannan kasuwancin ne domin mu sami riba.
“Mambobinmu suna fuskantar karin farashin a ma’aciyar man, sannan kuma suna shan wahala kafin su sami man.
“Idan akwai man, me zai sa ba za mu sayar ba, amma babu man me. Mambobinmu suna sayar da man a gidajen man kan naira 230 zuwa 240 kan kawacce lita daya,” in ji shi.
Mista Osatuyi ya ce gwamnati ta lura cewa zai yi mata wahala ta ci gaba da bayar da tallafin man wanda ya sa har ta sauya fasalin kamfanin man na kasa domin samun damar magance matsalar.
Ya bukaci gwamnati ta bar kamfanoni masu zaman kansu su dunga shigo da man fetur da dizil da kuma kalanzir. A cewarsa, cire hannun gwamnati wajen shigo da man shi ne zai bayar da damar cikakken hannanta bangaren man a hannun ‘yan kasuwa.