Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta soke shahararren auren da ake shirin gudanarwa tsakanin fitattun masu TikTok, Idris Mai Wushirya da Basira ‘Yar Guda, bayan da binciken hukumar ya gano cewa soyayyarsu ba ta gaskiya ba ce, illa dabara ce don su tsere wa hukunci na doka.
Mataimakin Kwamandan Hisbah, Dr. Mujahedeen Aminuddeen, ya bayyana a ranar Asabar cewa binciken cikin gida da hukumar ta gudanar ya nuna cewa babu niyyar aure ta gaskiya tsakanin masu yin TikTok ɗin. “Mun gano cewa wannan aure dabara ce kawai don gujewa matsalolin shari’a, don haka muka soke shi domin kaucewa rikice-rikicen gaba,” in ji shi ga manema labarai.
- Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
- Gwamnan Jigawa Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Tabbatar Da Hisbah
A cewarsa, an riga an kammala gwajin lafiya tsakanin ma’auratan kafin hukumar ta dakatar da shirin. Ya ƙara da cewa idan har ba a warware lamarin ba, akwai yiwuwar a dawo da shari’ar kotu. Tun da farko, Idris Mai Wushirya da Basira ‘Yar Guda sun gurfana a gaban kotun majistare ta Kano bisa zargin aikata abin da ya saɓa da tarbiyya, bayan da wani faifan bidiyo da ke ɗauke da su ya yaɗu a kafafen sada zumunta.
Alkalin kotun, Halima Wali, ta dakatar da yanke hukunci tare da miƙa shari’ar ga hukumar Hisbah domin ta tabbatar da an gudanar da aure bisa tsarin Musulunci, bayan da ma’auratan suka bayyana cewa suna soyayya kuma suna son aure. Kotun ta ba Hisbah wa’adin kwanaki 60 domin tabbatar da sahihancin aure.
Sai dai wannan hukunci ya haifar da muhawara a bainar jama’a, inda wasu suka soki kotun da zargin tilasta aure. Kakakin ma’aikatar shari’a ta jiha, Baba Jibo, ya ƙaryata hakan, yana mai cewa, “Kotun ba ta taɓa umartar tilasta aure ba. Abin da aka yi shi ne bayar da lokaci domin tabbatar da auren, tunda dukkansu sun bayyana cewa suna son juna.”
Ya ƙara da cewa Basira ‘Yar Guda ta bayyana cewa za ta amince da aure ne kawai idan Idris ya mallaki gidansa na kansa, ba wanda yake haya ba. Wannan ne ya sa kotu ta dakatar da yanke hukunci domin bai wa Hisbah damar tabbatar da cewa an bi tsarin aure yadda ya dace da shari’ar Musulunci.














