Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP Peter Obi, ya shelanta cewa ba zai binciki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba idan ya zama shugaban kasa a zaben 2023.
Ya sanar da hakan ne a jiya juma’a a Abuja a yayin da yake amsa tambayoyi bayan ya gabatar da Dakta Yusuf Datti Baba-Ahmed, a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a zaben na 2023.
- Garabasa Da Falalar Tsayuwar Arfa
- Kungiyoyin Sin Da Dama Sun Ba Da Ra’ayinsu Kan Hakkin Dan Adam A Rubuce Ga Majalisar Kare Hakkin Dan Adam Ta MDD
Obi ya kara da cewa, haka ba zai binciki shugabannin da suka shugabanci Nijeriya a baya ba.
Ya kara da cewa, zai yi dukkan mai yiwa domin ganin ya dakatar da cin hanci da rashawa a kasar nan, inda ya kara da cewa domin ba ta yadda za ka kulle shagonka ka ci gaba da bin barayi ba.
Ya bayyana cewa, wadanda suke yin dubi ga jiya da yau, za su rasa ganin gobe, inda ya kara da cewa domin Allah bai yi mana wani ido a keya ba
Ya sanar da cewa, idan yau ka shiga gidan gwamnati kuma ka ce za ta rufe wata kafa za ka samu wasu da dama kuma ni ba zan kasance shugaban da zai dinga munana wa wasu ba dole ne ‘yan Nijeriya su dinga bin doka da oda.
Obi ya yi nuni da cewa, Nijeriya a yau na fusknatar dimbin kalubale wadanda ba sai na fade su a nan ba.