An kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta kasashen Asiya karo na 19 wato Asian Games da daren ranar 23 ga watan Satumba a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, wanda ya kasance karo na uku da kasar ta karbi bakuncin gasar wasannin Asiya, bayan gudanar da irin ta a shekara ta 1990 a Beijing, da shekara ta 2010 a Guangzhou.
A matsayinta na gagarumar gasar wasannin motsa jiki ta kasashen Asiya, gasar tana hade da burikan al’ummun Asiya, a fannonin samar da zaman lafiya, da inganta hadin-gwiwa da nuna hakuri. A cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a wajen shagalin maraba da zuwan baki ‘yan kasashen waje na bikin bude gasar, ya bayyana fatansa ga gasar a wannan karo, wato tabbatar da zaman lafiya da karfafa hadin-gwiwa da kara nuna hakuri ta hanyar gudanar da wasannin motsa jiki. A shekaru goman da suka gabata, tattalin arzikin nahiyar Asiya ya habaka cikin sauri, wanda ya dauki kaso 40 bisa dari na tattalin arzikin duk duniya. Gasar wasannin Asiya ta ganewa idanunta gami da bayar da babbar gudummawa wajen kirkiro “al’ajabin Asiya”. Amma har yanzu akwai wasu kasashen sauran nahiyoyi, dake yunkurin tunzura rikici da lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Asiya, al’amarin ya sa al’ummun nahiyar suke matukar fatan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar gudanar da gasar wasannin motsa jiki. Ana iya cewa, gasar wasannin Asiya ta Hangzhou ta bana, na dauke da irin wannan fata na jama’ar nahiyar Asiya.
A tsawon kwanaki 16 na gasar, ba gagaruman gasanni kawai jama’a za su kalla ba, har ma za su iya kara fahimtar yadda ake kokarin inganta hadin-gwiwa da sada zumunta. Duba da cikakken goyon-bayan da al’ummun kasashen Asiya ke samarwa, babu shakka gasar wasannin Asiya ta Hangzhou za ta bayar da sabuwar gudummawa ga ci gaban gasar wasannin Olympics da karfafa hadin-gwiwa da zumunci tsakanin al’ummun kasashen Asiya. (Murtala Zhang)