Sakataren yada labarai na wucin gadi na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana dalilin da ya sa Peter Obi da Nasir El-Rufai ba su shigo cikin jam’iyyar hadaka ba ta ADC.
Abdullahi, a taron manema labarai a Abuja a karshen makon da ya gabata, ya bayyana cewa an ba Obi da El-Rufai damar kammala wasu ka’idojin zabe na cikin jam’iyyunsu na baya.
Ya tabbatar da cewa Obi da El-Rufai suna ci gaba da kasancewa tare da hadakar jam’iyyar ADC kuma za su shiga jam’iyyar a hukumance bayan kammala wadannan ka’idoji.
“An ba su damar kammala ka’idojin zabe da suka rage, ciki har da zaben cike gibi na ‘yan takarar majalisa a cikin jam’iyoyinsu na baya,” in ji shi.
A kan al’amuran cikin gida na jam’iyyar, Abdullahi ya ce ba su da wani shiri a boye ko wani dan Takara na musamman. Yana mai cewa kowa zai samu damar shiga gasar neman tikitin takara a jam’iyyar ba tare da wata matsala ba.
Mai magana da yawun jam’iyyar na wucin gadi ya ki janye ikirarinsa na cewa ADC na fuskantar manyan matsaloli a bangaren shari’a.
“Muna da tabbaci kan doka a kowane mataki da muka dauka. Mun tabbatar mun rufe duk wata baraka da jam’iyya mai mulki za ta iya amfani da ita a kanmu,” ya kara da cewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp