A daren ranar Laraba ne Gwamnatin Jihar Kano ta rushe shataletalen gidan gwamnati da Ganduje ya gina.
Sai dai cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba, ya ce gwamnatin ta tuntubi kwararru kan alfanun shataletalen, inda suka ce zai iya rushewa tsakanin 2023 zuwa 2024.
- Tinubu Ya Ba Da Umarnin Bincike Kan Hatsarin Jirgin Ruwan Kwara
- Daular Sakkwato Ta Buga Littattafan Malaman Musulunci Miliyan 3.2 —Sarkin Musulmi
Hakan ya sanya Gwamnatin ya hukuncin sake gina wani shataletalen da ya fi wannan inganci da nagarta.
Har ila yau, gwamnatin ta ce gina shataletalen a daf da gidan gwamnatin ya saba da tsarin tsaro wanda hakan ya sa ba a iya hangen abin da ke tahowa daga nesa.
Bugu da kari, yana haifar da cunkoson zirga-zirgar ababen hawa a wajen saboda girmansa, tare da toshe hanyoyin da masu ababen hawa ke fitowa.
Sanarwar ta ce gwamnati na son bayyana cewa ya zama dole a rushe shi domin sake gina wani cikin kankanin lokaci don saukaka jama’a da ke ta’ammali da hanyar.
Sai dai rushe shataletalen ya tada kura a kafafen sada zumunta, inda wasu ke bayyana bacin ran su ciki har da magoya bayan sabuwar gwamnatin ta NNPP.
Tun bayan karbar mulki da Abba Kabir Yusuf ya yi daga tsohon gwamnan Jihar Ganduje, ya shiga rusau na wasu gine-gine da ake zargin tsohon gwamnan ya sayar ba bisa ka’ida ba.