Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya kare ziyarar da gwamnonin Arewa suka yi zuwa kasar Amurka domin halartar taron tsaro.
Ku tuna cewa, gwamnonin sun sha suka sosai kan tafiya zuwa Amurka don tattaunawa kan lamuran tsaron cikin gida.
- NAF Ta Yi Barin Wuta A Maɓoyar ‘Yan Ta’adda Da Ke Neja
- Halin Da Mata Ke Shiga Sakamakon Rashin Samun Gamsuwa Daga Mazajensu
Sai dai da yake magana yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, a ranar Juma’a, Dikko Radda ya ce, sun yi tafiyar ne da nufin nemo mafita mai dorewa kan matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.
Ya ce, Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka ce ta gayyaci gwamnonin zuwa taron domin samar da mafita mai dorewa kan matsalolin da suka addabi jama’ar yankin.
Ya yi nuni da cewa, sun samo wata kyakkyawar fahimta bayan jin ta bakin kwararru wajen samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro a duniya.