Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya ce ‘yan siyasar da ke barin jam’iyyunsu suna komawa APC, na nuna cewa jam’iyyun adawa sun fara rauni kuma ba su da haɗin kai.
Da yake jawabi a Enugu lokacin taron karɓar Gwamna Peter Mbah da magoya bayansa zuwa APC, Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, ya ce wannan sauyi na nuna ƙarfin da haɗin kan da APC ke da shi.
- Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
- Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin
“Abin da jam’iyyun adawa suka kasa yi shi ne tambayar kansu dalilin da ya sa APC ta zama zaɓin mafi yawan ‘yan siyasa masu hangen nesa.
“Canjin da suke yi yana nuna giɓin da ke cikin jam’iyyunsu da kuma ƙarfafa gadar da muka gina,” in ji shi.
Shettima ya yaba da irin salon jagoranci na Shugaba Tinubu, yana cewa salon shugabancinsa na haɗin kai da gaskiya ne ya sa APC ta zama mafi ƙarfi a Afirka.
“Salon shugabancinsa da amincewa da cancanta sama da son rai ne ya sa kowane mai kishin ci gaba daga ƙarshe yake samun mafaka a APC,” in ji shi.
Gwamna Mbah ya bayyana shiga jam’iyyar APC bayan tattaunawa da magoya bayansa, yana mai cewa hakan “sabuwar tafiya ce” ga Jihar Enugu da yankin Kudu maso Gabas wajen samun babban matsayi a siyasar ƙasa.