Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta arewa, Ali Ndume, ya bayyana rashin amincewarsa da kudirin gyaran haraji, da ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa.
Da yake jawabi a matsayin bako a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels, tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawan ya soki lokacin da za aka bujiro da kudirin, yana mai cewa kamata ya yi a mayar da hankali kan gyara harkokin mulki kafin a sake fasalin haraji.
- Hukumar NDLEA Ta Kama Mutane 14,480 A Cikin Watanni 10 – Marwa
- Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudurinsa Na Bai Wa Ɓangaren Shari’a ‘Yanci Don Samar Da Adalci A Zamfara
An dai bayyana cewa majalisar dattawa ta amince da kudirin dokar haraji guda hudu a karatu na biyu a ranar Alhamis ta hanyar kada kuri’a.
Kudirorin sun hada da kudirin kafa hukumar tattara kudaden shiga ta hadin gwiwa, kotun daukaka kara ta haraji, da kuma ofishin mai kula da haraji, duk wani bangare na shirin sake fasalin haraji na Shugaban kasa Bola Tinubu.
Sai dai Sanata Ndume ya bayyana damuwarsa game da kudirorin, inda ya ba da misali da batutuwa irin su lokacin da bai dace ba, batun cire haraji, karin haraji, da kuma rashin amincewa daga wurin ‘yan Nijeriya.
Ya kuma bayyana cewa kasar na kashe sama da kashi 50 cikin 100 na kasafin kudinta wajen kashe kudade na yau da kullun da kuma biyan basussuka.
“Eh, yana da kyau a yi gyara. Amma ko da gyaran ne za a yi dole ne a ba da fifiko a lokacin da ya dace, kuma a tabbatar da ra’ayin ‘yan Nijeriya domin wannan dimokuradiyya ce. Gwamnati ce ta jama’a, wanda mutane suka zabeta da hannunsu.
“Na farko a Nijeriya abin da ya kamata mu yi shi ne gyara harkokin gwamnati. Ma’aikatanmu da kashe-kashen kudade marasa amfani da aka yi a kasafin kudin shekarar 2024, wanda aka kashe kusan kashi 50 zuwa 60 na kasafin kudin da kansa. Har zuwa Nuwamba kuma ba a aiwatar da kashi 20 na kasafin kudin ba. Amma idan ka duba kudaden da ake kashewa akai-akai, ya riga ya kare.
“Saboda haka, sama da naira tiriliyan 15 zuwa 20 ne ke shiga cikin ma’aikata, da biyan basussuka, da kuma kashe-kashe na yau da kullum. Ya kamata mu gyara gwamnati, ba kawai bangaren zartarwa ba, muna bukatar sake fasalin gwamnati gaba daya,” in ji shi.
Sanatan ya kuma nuna damuwarsa kan cewa, idan har ma ya zama doka, to majalisar dattawa ta dauke shi tamkar wani kudiri na shugaban kasa ne, wanda hakan ya zai kara karfafa zaman doya da manza tsakanin majalisar da bangren zartarwa.