‘Yan kasuwan man fetur sun bayyana cewa sun kara kudin kowacce litar man fetur zuwa naira 179 ne saboda bin umurnin Kamfanin man na kasa (NNPC).
Su dai ‘yan kasuwan man sun ce karin ya samu ne sakamakon bin umurnin Kamfanin NNPC, wanda ya janyo aka kai farashin zuwa naira 179 daga naira 165 a kan kowacce lita.
Bisa bin wannan umurni a yanzu an fara sayar da kowacce litar man fetur kan naira 179 maimakon naira 165 da ake sayarwa a baya, kuma karin ya fara ne daga tun daga ranar 19 ga watan Yulin 2022.
Bincike ya nuna cewa tun da aka fitar da wannan sanarwa wasu daga cikin ‘yan kasuwan man fetur suka juya akalar farashin nasu, musamman a buranan Legas da Abuja da sauran sassan kasar nan.