Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya, CDS Janar Christopher Musa ya bayyana dalilan da suka sa har yanzu ba a kawo karshen ta’addanci ba duk da dimbin kason kasafin kudin da ake ware wa sojoji duk shekara.
Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a daren ranar Talata, Janar Musa ya ce, sojoji ba su da isassun kayan aikin da za su yaki ‘yan ta’addan, domin a duk shekara ba a bayar da dukkan kudaden da aka ware wa bangaren tsaron.
- ‘Yansandan Sun Kama Masu Laifi 130 A Watan Nuwamba A Katsina
- Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Masu Maulidi A Kaduna
Ya kuma kara da cewa, jama’ar gari da ke hada kai da ‘yan ta’adda wajen sayo musu kayayyakin ta’addanci, na kara kawo cikas ga kokarin da sojoji ke yi na kawo karshen ‘yan ta’addan.
CDS ya bayyana haka ne yayin da yake magana kan harin Bam a ranar Lahadi da rundunar sojin saman Nijeriya ta kai a kauyen tudun biri da ke karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna. Akalla mutane 90 ne aka ruwaito sun mutu yayin da aka ce kusan mutane 60 sun jikkata.
Da yake magana kan dimbin kudin da ake ware wa bangaren tsaro amma kwalliya ba ta biyan kudin sabulu, CDS ya ce “akwai bambanci tsakanin abin da aka ware a kasafi da wanda ake baiwa bangaren tsaron.”