Kasa da watanni biyu kafin zaben 2023, Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, ya ce zai yi wuya a iya tafka magudin zabe.
Akeredolu, ya ce tunda aka bullo da tsarin tantance masu kada kuri’a na BVAS, yin magudi zai yi wahala.
- Da Hausa Ya Dace A Rinka Jawabi A Taron Mumbayya – Sule Lamido
- Ya Kamata Kasar Amurka Ta Biya Karin Diyya Ga Tsibiran Marshall
Ya bayyana haka ne a ofishinsa lokacin da ya karbi bakuncin kwamishinan zabe na jihar, Rufus Akeju (mai ritaya).
Gwamnan, ya bayyana bullo da BVAS a matsayin wani abin yabawa a harkar zabe a Nijeriya.
Akeredolu ya yaba wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), kan yadda ta samar da fasahar don karfafa tsarin zaben da kuma karfafa kwarin gwiwa.
Ya kara da cewa, bullo da fasahar zamani ya sanya yin magudi ya zama abu mak wahala, inda ya ce hakan zai tabbatar da cewa jam’iyyar APC za ta yi nasara a kowane zabe da ke tafe.
A cewar Akeredolu: “Na yi farin ciki zai yi wahala ga wani ya rinjayi INEC don yin magudin zabe. Na yi zabe da yawa, kuma ina gaya wa mutane cewa, zaben yana da wuya a yi magudi.
“Yanzu abu ne mai wahala, domin ko muna so ko ba mu so, INEC ta kara inganta ayyukanta a kan lokaci, kuma ina so na taya ku da shugaban kasa murnar wannan kyakkyawan aiki da kuka yi.”
Akeredolu ya yabawa shugaban saboda jihar ba ta taba yin zaben da bai kammala ba a lokacin da yake jagorantar jihar.