Rikicin da ya barke tsakanin manoma da Fulani makiyaya a kauyen Rogu da ke karamar hukumar Patigi a Jihar Kwara, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutum daya.
Leadership Hausa ta tattaro cewa biyo bayan mutuwar manomin, wasu Fulani manoma ne suka mamaye sansanin Fulani da ke kauyen.
- Dalilin Da Zai Yi Wuya A Yi Magudin Zabe A 2023 – Akeredolu
- Duk Wanda Ya Yake Ni Zai Gane Kurensa – Kwankwaso Ga Ganduje
Mamayar ta biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin manoma da Fulani makiyaya a kauyen.
Manoman sun yi zargin kona kadarori na Fulani makiyaya da suka hada da babura, kamar yadda rahotanni suka shaida wa Leadership Hausa.
Etsu Patigi, Alhaji Ibrahim Umar Bologi II, ya shiga cikin rikicin inda ya yi kira da al’ummarsa da su kwantar da hankalinsu tare da wanzar da zaman lafiya a yankin.
Ya kuma tabbatar wa Fulanin cewa babu wani ramuwar gayya da ‘yan uwansa za su yi, kuma babu abin da zai faru ga kowa, kamar yadda zaman lafiya ya samu a yankin.
Shugaban kungiyar Fulani ta Gan Allah reshen Jihar Kwara (GAFDAN), Ali Muhammed Jounwuro, a martanin da ya mayar a Ilorin a ranar Asabar, ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda aka kone akalla gidaje 103 na Fulanin da ba su ji ba ba su gani ba.
Ya tambayi dalilin da ya sa mutanen da aka zalunta su dauki doka a hannunsu idan suna zargin wasu suna aikata abin da bai dace ba.
Shugaban ya kara da cewa, “Rugar Fulani sun fi shekara 40 a Rogu da ke karamar hukumar Patigi, sun kasance masu bin doka da oda tsawon shekaru 40 ba tare da cutar da kowa ba.”
Ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kwara da ta dauki matakin da ya dace kan lamarin domin kaucewa barkewar rikici.